Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi ƙarin bayani kan kalaman da ya yi game da gwamnonin Arewa shida da suka mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya kafin ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen fidda gwani na 2022.
Shettima ya ce maganar tasa tana nufin ne kawai lokacin shawarwari da haɗin gwiwar siyasa da aka yi kafin zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a watan Yunin 2022. Ya ce ba yana nufin matsayin gwamnonin Arewa na APC ba ne bayan Tinubu ya zama ɗan takarar jam’iyyar.
Sanarwar da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce bayan Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani, gwamnonin APC na Arewa sun mara masa baya tare da taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen da ya kai ga nasararsa a zaɓen 2023.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana girmama gwamnonin Arewa da sauran shugabannin APC, tare da amincewa da irin gudunmawar da suka bayar wajen nasarar jam’iyyar da kuma samun nasarar Tinubu. Ya ce bai wai yana nufin nuna cewa gwamnonin ba su goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023 ba.
Shettima ya kuma yi nadamar duk wata fahimta da ta taso daga kalamansa wadda za ta iya nuna akasin hakan, yana mai cewa bayanin nasa na da nufin sanya kalaman cikin ainihin yanayin da aka yi su.
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da bayar da rahotanni cikin daidaito da cikakken muhallin da aka yi magana yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe mai zuwa.














