Kafin ziyarar aiki a Masar da shugaban Sin Xi Jinping zai yi, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya kaddamar da bikin nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na Sin masu inganci a birnin Cairo na Masar. An kuma watsa shirye-shirye kusan goma da CMG ya shirya a muhimman kafofin watsa labarai na kasar.
Shen Haixiong, shugaban CMG, ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce CMG da kafofin watsa labarai na Masar sun gudanar da wannan biki tare, wanda wani mataki ne na hakika na karfafa mu’amalar al’adu tsakanin kasashen biyu, da kuma karfafa tushen ra’ayin jama’a na sada zumunta tsakanin kasashen. Ya ce shirye-shirye masu inganci kamar “Wasikar Shugaba Xi”, “Sha’awar Xi Jinping ga al’adu”, “Yaya zamanantarwa iri ta Sin take”, “Lokacin da Fir’auna ya hadu da Sanxingdui”, da kuma “Fara tafiya daga Quanzhou”, suna ba mutane damar fahimtar tunanin da shugaban Sin Xi Jinping ke da shi wajen inganta zumunci da kuma mu’amala da juna tsakanin al’ummun kasashe, da kuma fahimtar hikimar al’adun Sin masu zurfi da kuma kuzarin Sin a sabon zamani.
Ya kara da cewa, CMG na son amfani da wannan dama wajen nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin masu inganci don yin hadin gwiwa sosai da kafofin watsa labaran Masar, da ci gaba da zurfafa musayar al’adu tsakanin Sin da Masar, da fadada yawan abokai na kafofin watsa labaran kasashen biyu, da kuma bayar da sabbin gudummawa wajen ci gaba da karfafa ma’anar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil’adama.
Bugu da kari, yayin da shugaba Xi Jinping zai yi ziyarar aiki a Kyrgyzstan, CMG zai kaddamar da bikin nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na Sin masu inganci a lokacin. (Safiyah Ma)














