ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga 1930 Zuwa 2026: Yadda Aka Buga Wasa Na Dubu Ɗaya A Gasar Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada and Sulaiman
3 weeks ago
Kofin Duniya

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA mai tsara gasar cin kofin duniya, ta gabatar da wani wasan da ya shiga kundin tarihinta. Wannan wasan shi ne tsakanin Tunisia da Japan wanda ya zama wasa na 1,000 a babbar gasar ta duniya.

Ƙasashen sun kece raini ne a wasan cikin rukuni na shida da za su fafata a katafaren filin wasa da ke Monterrey a Meɗico. A tarihin gasar cin kofin duniya ta FIFA, akwai wasu wasanni da ba a mantawa da su. Amma a gasar FIFA World Cup 2026, an kafa wani babban tarihi mai matuƙar muhimmanci — wasa na 1,000 a tarihin gasar.

Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta fara ne a shekarar 1930 a Uruguay, inda aka buga wasanni kaɗan, idan aka kwatanta da wadda ake yi a bana. A wancan lokaci, ƙasashe ƙalilan ne ke shiga gasar.

ADVERTISEMENT

Amma a tsawon shekaru, sai gasar ta faɗaɗa daga ƴan ƙalilan tawaga zuwa 13 daga nan suka koma 32, sannan yanzu ƙasashe 48 ke kece raini a gasar 2026.

Yawan wasanni ya ƙaru sosai, saboda ƙarin ƙasashe da sabon tsarin wasannin cikin rukuni zuwa zagaye na biyu kai har ta kai ga wasan ƙarshe.

LABARAI MASU NASABA

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Wannan ci gaba ne ya sa aka kai ga adadin wasanni da ya haura 999, sannan wasa na 1,000 zai zo a wannan gasar ta 2026 da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Meɗico.

A cewar rahotanni na FIFA, wannan wasa na tarihi zai gudana a Estadio BBDA TAKWARARTAA, Monterrey, inda Tunisia da Japan za su kara domin rubuta suna a littafin tarihi.

Wasan yana da abubuwa da suka sa ya zama na musamman

1. Yawan wasan da ake buga wa

Ba kowace rana ba ce ake kaiwa wasa 1,000 a gasar duniya. Wannan yana nuna tsawon tarihin gasar da ci gaban da ta samu da kuma girmanta.

2. Ƙasashen daban-daban

Tunisia daga Afirka take, Japan kuma daga Asiya take wakilta. Wannan yana nuna yadda wasannin gasar cin kofin duniya ke haɗa tawaga daga nahiyoyin duniya, domin tantance gwana daga ƙarshe.

3. Filin wasa na zamani

Wasan ya gudana ne a filin wasa na Monterrey a Meɗico, ɗaya daga cikin sabbin wuraren da ke karda takwararta baƙuncin gasar cin kofin duniya a 2026 na gani na faɗa mai ɗauke da kayayyakin zamanin.

Taƙaitaccen tarihin FIFA World Cup

An fara a 1930

Brazil ce kasa mafi yawan lashe kofin. Ƙasashe sama da 80 sun tada takwarartaa shiga gasar tun fara ta.

Yanzu tana ɗaya daga cikin manyan wasannin da ake fi kallo a duniya. A tsawon wannan lokaci, an buga ɗaruruwan wasanni masu tarihi — amma wasa na 1,000 zai zama wani sabon babi mai muhimmanci.ages

Yadda aka fara wasan farko zuwa na 1,000 da aka buga

A cewar FIFA, an riga an tantance wasu muhimman wasannin tarihi, yayin da za a buga fafatawa ta 1,000 a gasar kofin duniya. Ga bayanan da aka tattara:

 Wasa na farko (1) France 4-1 Meɗico da kuma Amurka 3-0 Belgium (an fara su lokaci guda a ranar 13 Yuli 1930).

Wasa na 500

Wasannin ƙarshe a rukuni na huɗu a gasar 1994, inda Nijeriya da Bulgaria da Argentina suka kai zagaye na gaba. FIFA ta ayyana wannan rana a matsayin wasa na 500 a tarihin gasar.

Wasa na 900

Wasan ƙarshen gasar 2018 tsakanin France da Croatia (Faransa ta ci 4-2). FIFA ta bayyana wannan a matsayin wasa na 900 a tarihin gasar.

Wasa na 999

Netherlands da Sweden a rukuni na shida, kafin Tunisia da Japan.

Wasa na 1,000 Tunisia da Japan a Monterrey, Meɗico, ranar 20 Yuni 2026.

Alƙalain wasa Koda takwarartaacs ne ya jagoranci wasa na 1,000

Alƙalin  wasa ɗan ƙasar Romania, Istda takwarartaán Koda takwarartaács, shi ne ya busa wasa na 1,000 a tarihin gasar Kofin Duniya ta FIFA, wanda zai kasance karawar rukuni na shida tsakanin Tunisia da Japan a filin wasa na Monterrey ranar Asabar, 20 ga watan Yuni.

Koda takwarartaács mai shekara 40 zai yi alƙalancin karawar tare da taimakon takwarorinsa ƴan ƙasar Romania, Ferencz Tunyogi da Mihai Marica. Haka kuma, Juan Calderon da Juan Carlos Mora daga Costa Rica za su kasance alƙalin wasa na huɗu da kuma mai jiran ko ta kwana.

Wasan yana daga cikin fitatciyar karawa da ta shiga tarihi a wannan gasa mai ɗimbin tarihi da daraja. A farkon wannan shekarar ranar 31 ga watan Mayu, Koda takwarartaács ne ya yi alƙalancin wasan ƙarshe a UEFA Champions League tsakanin Paris Saint-Germain da Inter Milan a Munich.

Haka kuma, ya jagoranci wasan ƙarshe a Europa Conference League a shekarar 2022, sannan shi ne alƙalin wasan ƙarshe a Europa League a 2024 tsakanin Atalanta da Bayer Leda takwarartaerkusen. Naɗin Koda takwarartaács domin wannan wasa mai tarihi ya nuna irin amincewar da FIFA ke da ita a kansa da ƙwarewarsa a manyan wasannin ƙwallon ƙafa na duniya.

Wasa na dubu ɗaya a gasar cin kofin duniya ba kawai game da Tunisia ko Japan ba ne. Yana nuna:

Yadda ƙwallon ƙafa ke haɗa al’ummomi, yana nuna yadda gasar ta girma daga ƙarama zuwa babba a duniya. Wasan ya nuna yadda ake ci gaba da kafa tarihi da yin abubuwan bajinta duk bayan shekara huɗu. Ga magoya bayan ƙwallon ƙafa kuma,wasan ya zama lokacin tunawa, wanda za a daɗe ana magana akai.

Kofin Duniya
Abba Ibrahim Wada
Website |  + posts Bio
  • Abba Ibrahim Wada
    Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji
Kofin Duniya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing
  • Sulaiman
    Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri
  • Sulaiman
    Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK
  • Sulaiman
    Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

MASU ALAKA

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya
Wasanni

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

July 18, 2026
Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi
Manyan Labarai

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

July 17, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL
Wasanni

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Next Post
Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

Tsarin Kirkire-Kirkire Na Sin Na Kara Kuzari Ga Makomar Masana’antun Duniya

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta

July 18, 2026
Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

Xi Jinping Ya Bukaci A Gudanar Da Aikin Ceto A Tsanake Bayan Rugujewar Bangaren Wani Tsauni A Chongqing

July 18, 2026
Yadda Ake Miyar Karkashi Da Nama

Yadda Ake Miyar Karkashi Da Nama

July 18, 2026
Kura-kurai 7 Da Mata Ke Yi Wajen Kula Da Fatarsu

Kura-kurai 7 Da Mata Ke Yi Wajen Kula Da Fatarsu

July 18, 2026
Majalisa Ta Goyi Bayan CBN Kan Sauya Fasalin Naira Bayan Tafka Muhawara 

Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar MDD Ta Bincikar Badakalar Satar Daliban Oyo

July 18, 2026
Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

July 18, 2026
Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

July 18, 2026
Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

July 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.