ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Dakatar Da Jarumai Zuwa Dakatar Da Bukukuwan Biki: Tasirin Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano

by Sulaiman
1 month ago
Kano

A kwanakin baya hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da wasu daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa bayan an ɗaura aure da sauran tarurrukan biki da ake gudanarwa a cibiyoyin manyan taruka a faɗin jihar, Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, shi ya sanar da dakatarwar a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abdullahi Sulaiman, ya fitar.

A cewar sanarwar, matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da hukumar ke yi na tabbatar da bin ƙa’idoji da kula da ayyukan manyan cibiyoyin taruka a faɗin jihar, El Mustapha ya ce an janyo hankalin hukumar dangane da irin waɗannan tarukan da ake gudanarwa waɗanda kuma suka ci karo da koyarwar addini, da kuma al’adun al’ummar Jihar Kano, inda ya ƙara da cewa mafi yawancin tarukan ana kwaikwayon ƙasashen turawa wajen aiwatar da su.

“Saboda haka, hukumar ta dakatar da wannan tarukan domin kare al’adu, ɗabi’u da addini na mutanen Jihar Kano,” in ji sanarwar.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar, wannan matakin da hukumar ta ɗauka ya zama dole a matsayin wani ɓangare na aikin hukumar wajen tsaftace ayyukan nishaɗi da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da tarurrukan jama’a daidai da ƙa’idodin al’adu da addini na jihar.

Sanarwar ta jaddada cewa hukumar tana maraba da duk wani nau’in nishaɗi wanda zai ƙayatar a bukukuwan aure da sauran tarurrukan zamantakewa, muddin sun inganta ɗabi’a tare da girmama al’adun mutane da kuma bin koyarwar addini. A cikin sanarwar an ce hukumar ta ce nishaɗi ya kasance muhimmin ɓangare na bukukuwa idan aka gudanar da su bisa ƙa’idojin ɗabi’un da aka amince da su.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Hukumar ta ƙara da umurtar dukkan cibiyoyin tarurruka, masu jagorantar taruka (MC) da sauran masu ruwa da tsaki da ke da hannu a shirya tarurruka, da su bi umarnin da aka gindaya masu, tana mai gargaɗin cewa duk wani mutum ko ƙungiya da aka samu da karya wannan dakatarwar na iya fuskantar hukuncin da ya dace bisa ga dokokin da hukumar ta tanada, hukumar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su goyi bayan ƙoƙarinta ta hanyar bayar da rahoton duk wani taro ko MC da aka samu yana karya doka ko kuma aiwatar da ɗaya daga cikin ayyukan da aka dakatar.

Kano
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Kano
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
Labarai

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Next Post
Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Kassara Wasu Kamfanonin Kasar Ta Fakewa Da Batun Kwadagon Tilas

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Kano

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Kano

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.