Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya bayyana matukar Allah-wadai, da sukar manufar gwamnatin Amurka, ta sanya karin sassan kasar Sin 40, cikin jadawalin da ta kira na “Kudurin dakile kwadagon tilas tsakanin ‘yan Uyghur.”
A cewar kakakin, matakin Amurkan ba shi da tushe ko kadan, duba da yadda aka yi amfani da batun “Kare hakkin bil’adama”, da “Kwadagon tilas”, wajen kakabawa kamfanonin kasar Sin tarnaki bisa dokokin gidan Amurka.
Kakakin ya kara da cewa, irin wadannan matakai ba komai ba ne illa matsayin lamba irin na tattalin arziki. Ya ce matakan na Amurka, sun yi matukar keta hakkoki da moriyar kasar Sin, sun kuma illata daidaitaccen tsarin ayyukan masana’antun duniya.
A lokaci guda, har kullum kasar Sin na adawa da kwadagon tilas, kuma a halin yanzu, jihar Xinjiang ta kasar Sin na cin gajiyar madaidaicin tsarin zamantakewa, da bunkasar tattalin arziki, da zaman lumana tsakanin al’ummunta, kuma babu wani batu na tilasawa jama’a yin kwadago a jihar. (Saminu Alhassan)














