Tun farkon wannan shekara, lokacin da aka fara aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15 da kyau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yanke jerin manyan shawarwari tare da fitar da jerin tsare-tsare kan kirkire-kirkire na fasaha, don gaggauta dogaro da kai a fagen fasaha.
“Ci gaban fasaha na dogaro da sauri da fadi da kuma zurfin ci gaban masana’antu na zamani”, kamar yadda Shugaba Xi ya bayyana a lokacin da yake jagorantar taron kara wa juna sani na farko na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin (JKS), inda ya jaddada wajibcin samun ci gaban masana’antu na zamani, bisa hangen nesa na farfado da al’ummar Sinawa bisa la’akari da yanayin da ake ciki, kana da amfani da fa’idoji da fifikonta don samun ci gaba ba tare da tangarda ba, don bunkasa masana’antu a matakai daban-daban. (Amina Xu)














