ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussan Koyo Daga Salon Bunkasa Kasa Na JKS

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
Jks

Yayin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko JKS ke ciki shekaru 105 da kafuwa, masharhanta na ta bayyana ra’ayoyinsu dangane da gagarumar gudunmawa da jam’iyyar ta bayar a fannin bunkasa ci gaban kasar Sin, irin ci gaban da ya zamo mai matukar ban mamaki da kayatarwa.

Ko shakka babu JKS ta dora kasar Sin kan turbar ci gaba mai inganci, kuma mai dacewa da yanayin da kasar ke ciki, ta kuma samar da wani kyakkyawan misali na yadda kasashe daban daban, musamman masu tasowa za su iya zabar turbar ci gaba mafi dacewa da yanayin da suke ciki maimakon koyi ido rufe daga wasu sassa na daban. A kasar Sin JKS ta samar da nata manufofi masu nagarta, wadanda suka dace da yanayin kasar Sin, an kuma ci gaba da aiwatar da sauye-sauye kan tsare-tsaren wucin gadi, kafin aiwatar da manufofi masu game dukkanin kasa. Ta haka ne kuma kasar Sin ta kai ga kafa manyan tsare-tsaren raya kasa masu dacewa da al’ummunta.

Kamar yadda shaidun zahiri suka nuna, karkashin jagorancin JKS, kasar Sin ta yi nasarar bunkasa tattalin arziki, da daidaita yanayin zamantakewar al’ummun kasar yadda ya kamata. Inda a yanzu al’ummun kasar ke cin gajiyar nasarori masu dorewa.

ADVERTISEMENT

A bangaren zamanantar da kasa, baya ga samar da manufoin farfado da kasar Sin, JKS ta kuma jagoranci sabbin hanyoyi na ingiza ci gaba, irin wadanda tabbas sauran kasashe masu tasowa, kamar na Larabawa da na nahiyar Afirka za su iya koyi da su wajen cimma nasu nasarorin. A zahirin gaskiya, JKS ta wanzar da karsashi, da karbuwa tsakanin al’ummun kasar Sin, kuma dalilin hakan shi ne yadda ta mayar da burikan jama’a gaban komai. JKS ta jagoranci tsame kusan mutum miliyan 100 daga kangin matsanancin talauci, tare da kafa tsarin kiyaye walwalar jama’a mafi girma da nagarta a duniya.

Wasu karin fannoni da JKS ta yi fice sun hada da kyautata jagoranci, da karfafa da’a, da ingiza nagartar aiki, da yaki da cin hanci da rashawa, wasu dabi’u suka taimaka wajen inganta ikon jam’iyyar na samar da shugabanci na gari da karfafa gwiwar jami’ai a dukkanin matakai.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Yayin da kasar Sin ke kara samun ci gaba karkashin jagorancin JKS, tana kuma karfafa hadin gwiwa da sauran sassa, bisa kudurorin hadin kai daban daban, irin su dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da shawarar ziri daya da hanya daya da sauransu, wadanda kawo yanzu ke ta haifar da gajiya ta fannin samar da ababen more rayuwa, da makamashi da sauran muhimman fannoni.

Bahaushe kan ce, “Yabon gwani ya zama dole”, JKS ta yi an gani… kuma kwarewa, da gogewarta wajen samar da jagoranci mai nagarta da dorewa, ya zamo kyakkyawan abun koyi ga dukkanin kasashen duniya musamman masu tasowa, wadanda ke fatan saita akalar neman nasara bisa hakikanin halin da suke ciki. (Saminu Alhassan)

Jks
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Jks
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara
  • Sulaiman
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

MASU ALAKA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
Daga Birnin Sin

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Next Post
Binciken Ra’ayin Jama’a Na Duniya: Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin Jagora Ce Mai Karfi

Binciken Ra'ayin Jama'a Na Duniya: Jam'iyyar Kwaminis Ta Sin Jagora Ce Mai Karfi

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.