ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

by Sulaiman
2 months ago
Dauda Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta dawo da masana’antar yadi da kuma bunƙasa noman auduga a jihar, bayan ziyarar da ya kai Yankin Masana’antu na Glo-Djigbe (GDIZ) da ke Jamhuriyar Benin tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni.

Da yake jawabi bayan zagayen duba cibiyar masana’antun, Dauda Lawal ya ce abin da ya gani ya tuna masa da lokacin da masana’antar yadi ta Zamfara ke ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana cewa, ya taso ne a cikin yanayin wannan masana’anta, yana mai cewa mahaifinsa na daga cikin masu mallakar Masana’antar Yadi ta Zamfara, wadda a lokacin take gudanar da aiki sau uku a rana, inda kowane rukuni ke ɗaukar ma’aikata kusan 2,000.

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya ƙara da cewa, a wancan lokaci Zamfara na da masana’antun tace auduga guda 23 da kuma masana’antar sarrafa man auduga, inda har tsabar auduga ake sarrafawa zuwa man girki.

A cewarsa, nasarar da ya gani a yankin masana’antun na Glo-Djigbe ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen dawo da sarkar darajar auduga gaba ɗaya, daga noma zuwa sarrafawa da kuma samar da kayayyakin yadi a Zamfara.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

“Wannan ziyara ta nuna min hanya a fili. Dawo da wannan masana’anta na ɗaya daga cikin abubuwan da nake son bari a matsayin gadon mulkina a Zamfara, kuma na ƙuduri aniyar tabbatar da hakan,” inji Lawal.

Ya bayyana cewa farfaɗo da masana’antar auduga da yadi ba wai kawai zai ƙarfafa manoma ba ne, har ma zai buɗe damammakin kasuwanci ga masu sarrafa kayayyaki da masana’antun cikin gida, tare da samar da dubban guraben aikin yi da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ziyarar ta kasance wani ɓangare na shirin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa cibiyoyin sarrafa kayayyakin noma a sassa daban-daban na Nijeriya domin bunƙasa masana’antu da ƙara darajar albarkatun ƙasa.

Dauda Lawal
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.