ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

“Dokar Dakile Kwadagon Tilas Na ’Yan Uyghur”: Jama’ar Duniya Za Su Iya Bambance Gaskiya Da Akasinta

by Sulaiman
1 month ago
Uyghur

Kungiyar masana’antun auduga ta kasar Sin ta kalubalanci matakin Amurka na baya-bayan nan, na sanya karin kamfanonin kasar Sin 43, ciki har da kamfanonin sarrafa auduga, cikin jadawalin da ta kira na “Dokar dakile kwadagon tilas na ’yan Uyghur”.

An shafe shekaru da dama, Amurka tana sake sabunta matakanta na fakewa da batun hakkin dan Adam wajen kakaba wa kamfanonin Sin takunkumai, tana cewa ana tilastawa ’yan kabilar Ugyur kwadago.

Amma abun tambaya a nan shi ne, shin Amurka tana da kwararan shaidu dake tabbatar da hakan? Shin takunkuman da take kakaba wa na dogaro ne da sabbin shaidun da take samu ko kuwa? Ko bambancin ra’ayi kan tsarin tafiyar da harkokin kasa ya zama laifi? A wannan zamani da Sin ke kan gaba wajen kirkirowa da amfani da fasahohi da kayayyakin aiki na zamani a duniya, me zai sa ta nace wajen tilasta kwadago bayan tana da karfin samar da kayayyakin da za su iya rubanya kokarin dan adam fiye da sau 10? Abun da zai bayar da mamaki shi ne, ko a da can da aka fi amfani da jama’a wajen aiwatar da ayyuka, mutane da dama daga sassan kasar Sin ne ke zuwa jihar Xinjiang a lokacin girbin auduga domin shiga aikin don samun kudin shiga. Yayin wata ziyarar da na yi a jihar, na samu damar tattauna da wasu mutane da suka shaida min bisa radin kansu cewa, asalinsu ba ’yan jihar ba ne, kuma aikin girbin auduga ne ya sa iyayensu kaura zuwa jihar Xinjiang.

ADVERTISEMENT

To su da suka fito daga sauran sassan kasar Sin, tilasta musu aka yi?Ya kamata masu neman dakile ci gaban Sin ko son dusashe haskenta su fahimci cewa, hakar su ba za ta cimma ruwa ba, domin kasar Sin na fadada bude kofarta ga kasa da kasa.

Kuma a yanzu duniya tana tafin hannun jama’a. Kafafen yada labarai masu tsare gaskiya da kafofin sada zumunta na kara wayar da kan al’umma game da ainihin yanayin da ake ciki, kuma za su iya bambance gaskiya da akasinta. (Faeza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Uyghur
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
Uyghur

An Yanke Wa Wani Saurayi Hukuncin Kisa Bayan Ya Kashe Abokinsa A Kano

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.