Wata shari’ar kisan kai tazo ƙarshe a Jihar Kano yayin da Babbar Kotun Jihar ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani saurayi mai suna Jamilu Eruda, biyo bayan samun sa da laifin gudanar da ɗanyen aiki na soka wa abokinsa wuƙa har lahira.
Hukuncin ya fito ne daga bakin Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, inda ya tabbatar da cewa dukkan hujjoji da shaidun da aka gabatar a gaban kotun sun gamsar ba tare da shakko ba cewa wanda ake zargin shi ne ya aikata kisan kai ba.
Kamar yadda cikakken rahoton labarin ya bayyana, lamarin ya auku ne a unguwar Sabon Gari da ke ƙwaryar birnin Kano, sakamakon wani saɓani da ya ke tsakanin Jamilu Eruda da abokinsa marigayi Sani Abdullahi.
A lokacin gudanar da shari’ar, Lauyan Gwamnati daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Laminu Aliyu, ya bayyana cewa wanda ake zargi ya yi amfani da wuƙa mai kaifi ne inda ya soka wa marigayin a ƙirji, lamarin da ya sa numfashinsa ya katse a take kafin a kai shi asibiti.
Yayin da yake yanke shari’ar, Mai Shari’a Ma’aji ya jaddada cewa laifin kisan kai da gangan a ƙarkashin Sashi na 221 na Kundin Hukunta Laifuka na Jihar Kano ba ya ɗaukar rangwame, inda doka ta gindaya hukuncin kisa kaɗai ga dukkan wanda aka samu da laifin.














