Yau Litinin da rana, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Jiang Bin, ya yi tsokaci game da wasu batutuwan da suka shafi ayyukan soji na baya-bayan nan. Da yake tsokaci game da atisayen soji na hadin gwiwa tsakanin Japan da Amurka da Australia, a wurare daban-daban na Japan, wanda a karon farko na’urar harba da kakkabo makami mai linzami mai cin matsakaicin zango na Typhon na Amurka za ta halarta, Jiang Bin ya ce irin wadannan atisaye na da nufin kara jibge manyan makamai da yin barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin, kuma kasar Sin na matukar adawa da shi.
Ya ce duk wani yunkuri na kara karfafa burin Japan na fadada karfin soji, zai jefa yankin cikin yanayi mai hadari kuma ba makawa mummunan tasirinsa zai koma ne kan wadanda suka kitsa shi.
Jiang Bin ya kuma sanar da cewa, za a bude taron dandalin tattauna harkokin tsaro na kasa da kasa na Xiangshan na birnin Beijing a ranar 15 ga wata. Kuma wakilai daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa kusan 100 ne za su halarci taron na bana. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














