ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

by Sulaiman
52 minutes ago
BRICS

A karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da taron kolin kungiyar BRICS ta kasashe maso saurin samun ci gaba, a birnin New Delhi na kasar India. Yayin taron a ranar Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, wanda ya yi kira ga kungiyar da ta mayar da hankali kan wasu muhimman batutuwa 4.

Da farko dai, babban sakon dake tattare da taron shi ne, kasashe masu tasowa su tashi daga wadanda ake juyawa, zuwa wadanda ake damawa da su cikin harkokin duniya. Watau su sauya daga masu karba ko wadanda ake ba umarni da kakaba wa ka’idoji da dokoki, zuwa wadanda ke da karfin fada a ji, inda su ma za su rika shiga cikin harkokin shugabantar duniya da tafiyar da harkoki da samun ci gaba da tafiyar da harkokinsu na cikin gida da kansu.

Tasirin kungiyar BRICS na karuwa a duniya la’akari da yadda kasashen kungiyar suka dauki kaso 40 na alkaluman GDP na duniya da kaso 49.5 na al’ummar duniya.

ADVERTISEMENT

Idan muka nazarci batutuwa 4 da shugaban kasar Sin ya gabatar, to a dunkule, mafita ce ga matsalolin da duniya ke fuskanta.Shugaba Xi ya bukaci su zama jagororin samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire. Yanayin duniya ya sauya zuwa fasahar zamani, don haka, ya kamata kasashen su tashi tsaye su jagoranci bangaren domin kada a bar su a baya. Idan suka kasance masu tsayawa da kafarsu a bangaren, to za su amfani duniya da jama’arsu, haka kuma za su sauya salon duniya na danniya da babakere.Na biyu ya bukaci su jagoranci tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Tsarin huldar BRICS shi ne girmama juna da hadin gwiwa bisa adalci da daidaito, wanda wata ingantacciyar hanya ce ta tabbatar da zaman lafiya, sabanin tsohon tsarin yammacin duniya na fin karfi da cin zali, wanda ke haifar da tashe-tashen hankula. Akwai bukatar kasashen masu tasiri a duniya, su tsaya kai da fata wajen adawa da cin zali domin a samu duniya mai zaman lafiya da kwanciyar hankali.Na uku, su zama masu bunkasa koyi da juna tsakanin mabambantan al’ummomi.

LABARAI MASU NASABA

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

Fahimtar juna na da matukar muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin kasa da kasa. Ba za a samu fahimtar juna ba, har sai an yi mu’amala, an gane al’adu da mabambantan halayyar juna. Wannan shi zai yi maganin masu yada karairayi da jita-jita da dakile gadon adawa tsakanin mabambantan al’ummomi. Na hudu, su jagoranci inganta tsarin shugabancin duniya.

Tabbas idan muka duba tafarkin da ake kai yanzu, to wasu ’yan tsiraru masu arziki ne ke juya duniya bisa son ransu. Sai dai, yanzu akwai tarin kasashe masu tasowa, kuma kan duniya ya waye. Kowacce kasa na da yanayin da ya dace da ita da ya bambanta da na sauran. Don haka, akwai bukatar sauya tsarin shugabancin duniya ta yadda za a samu rarrabuwar iko tsakanin kasa da kasa da kara kyautata mu’amala tsakanin kasashe, maimakon kafa wasu kananan rukunoni, domin kara dunkule tattalin arzikin duniya.

Makomar dukkan dan adam hade suke da juna. Babu kasar da za ta iya ware kanta kuma ta samu ci gaban da take bukata, don haka jawabin na shugaba Xi, da manufofi da burikan kungiyar BRICS, su ne za su kawo mafita ga matsalolin da ake fuskanta da kuma samar da alkiblar wanzar da ci gaba da zaman lafiya da daidaito a duniya. (Faeza Mustapha)

BRICS
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu
  • Sulaiman
    Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

MASU ALAKA

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
Daga Birnin Sin

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

September 14, 2026
Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

September 14, 2026
BRICS

Babu Dalilin Da Zai Sa Nijeriya Yin Talauci – Obasanjo

September 14, 2026
Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya

September 14, 2026
BRICS

Air Peace Da United Nigeria, Jirage 2 Masu Latti Sosai Watan Agusta — NCAA

September 14, 2026
Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.