Fasahar kirkirarriyar basira ko AI, a matsayin wata fasaha mai muhimmanci ga makomar dan Adam, tana da tasiri sosai a rayuwarmu. Yanzu haka, abun da ake yawan tattaunawa a kai ya wuce yadda za a raya wannan fasaha, har ma ya fara shafar maganar wa zai sarrafa fasahar, da wa zai amfana da ita, da kuma yadda za a raba damar da take bayarwa daidai gwargwado.
A wannan fanni, kasar Sin, bisa matsayinta na daya daga cikin kasashe dake kan gaba a duniya a fannin raya fasahar AI da masana’antu masu alaka da ita, ta yanke shawarar raba damammaki tare da sauran kasashe.
A taron shugabannin kungiyar BRICS da aka kammala kwanan nan a kasar Indiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar samar da budadden tsarin fasahar AI da amfani da fasahar wajen samar da alfanu ga kowa. Shugaban ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta zama mambar kungiyar BRICS ta farko da za ta gina yankin musamman na samar da budadden tsarin AI a karkashin tsarin kungiyar, kana kasar za ta goyi bayan hadin gwiwar da ake yi wajen bunkasa da amfani da tsarin AI mai tunani, da samar da damammaki na horaswa game da ilimin fasahar AI, da kuma gina wani cikakken tsarin AI da kowa zai iya amfani da shi.
Wannan ba shi ne karo na farko da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana matsayin kasar Sin kan fasahar AI ba. A taron fasahar AI da ya gudana a birnin Shanghai na kasar Sin a watan Yulin bana, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken “A Hada Gwiwa Don Gina Tsarin Kula Da Fasahar AI Mai Adalci A Duniya”.
Dangane da wannan jawabi, Dr. Ebute Ugbedeojo, wanda ke aiki a cibiyar nazarin batutuwan tsaro ta kasar Najeriya, ya yi tsokaci cewa, “Shugaba Xi Jinping ba ya neman sanya fasahar AI zama dandalin takara na kasashe daban daban, maimakon haka, yana neman karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, da more sakamakon kirkire-kirkire a tsakaninsu, da kuma sanya karin kasashe masu tasowa su shiga a dama da su.” Ya ce shawarwarin kasar Sin suna ba da damammaki masu muhimmanci ga Najeriya, da sauran kasashe dake nahiyar Afirka, har ma da dukkan kasashe masu tasowa.
Baya ga alkawuran da ta dauka, kasar Sin tun tuni ta fara kokarin kafa wani budadden tsari ga fasahar AI, da neman daukar matakan da za su amfanar da kowa. Yanzu haka, yayin da ake fuskantar dubban harsuna, da kuma bukatu na musamman a fannin aikin gona, da ilimi, da kiwon lafiya, da aikin samar da hidimomi ga jama’a a nahiyar Afirka, karin kamfanoni masu sarrafa fasahar AI na kasashen Afirka na yanke shawarar amfani da fasahar AI kirar kasar Sin, mai kunshe da wani budadden tsari, wajen tsara manhajojin da suke bukata, ta yadda za a samar da hidimomi mafi inganci ga jama’a.
Kana a fannin kula da fasahar AI, kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da kafuwar kungiyar hadin gwiwa ta duniya a fannin fasahar AI, da wani tsarin kula da fasahar, wanda ke wakiltar ra’ayoyin mafi yawan kasashe. Bugu da kari, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen neman cimma matsaya daya a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, ta yadda aka fara mai da aikin taimaka wa kasashe masu tasowa wajen raya fasahar AI cikin manyan batutuwa masu alaka da kulawa da tsarin fasahar AI a duniya.
Me ya sa kasar Sin ke neman kafa budadden tsari na fasahar AI, da sanya ta amfanar da kowa? Saboda wannan mataki ya dace da babbar manufar kasar Sin ta kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. A ganin kasar Sin, ya kamata a yi kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa, da tsaro na bai daya, da wadatar da ta game sassa daban daban, a duniyarmu.
Saboda haka, bai kamata a bari wasu kasashe masu sukuni su yi babakere a fannin fasahar AI ba, ganin yadda hakan zai mai da AI wani shinge na fasaha da ake amfani da shi wajen kiyayewa ko ma fadada gibi tsakanin mabambantan kasashe ta fuskar ci gaban tattalin arziki. Maimakon haka, ya kamata a taimaki kasashe masu tasowa samun cikakken karfin raya kansu, da amfani da fasahar AI wajen tabbatar da ci gaba na bai daya ga kasashe daban daban. (Bello Wang)














