An gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS karo na 18 a birnin New Delhi na kasar Indiya daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Satumba da muke ciki. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron mataki na farko da na biyu kuma ya gabatar da muhimmin jawabi, inda ya yi kira ga kasashen BRICS da su zama abin koyi a bangaren inganta kirkire-kirkire da ci gaba, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da ciyar da musayar wayewar kai gaba, da kuma gyarawa da inganta tsarin shugabancin duniya.
Ya kuma gabatar da muhimman shawarwari 4 game da inganta karfin kasashe masu tasowa, wato kare dokokin kasa da kasa, da tsayawa ga inganta cudanyar mabambantan bangarori a duniya, da dagewa ga mayar da muradun jama’a a gaban komai yayin da ake samar da ci gaba, tare kuma da hada kai wajen daidaita ayyukan tsaro. Bugu da kari, ya gabatar da wasu shawarwari 5 game da zurfafa hadin gwiwar BRICS, al’amarin da ya shaida babban nauyin da ke wuyan kasar Sin na jagorantar samar da ingantaccen ci gaban bisa tsarin hadin gwiwar BRICS.
Wani masanin harkokin siyasa na kasar Sifaniya Rafael de Moura yana ganin cewa, shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar don karfafa kasashe masu tasowa da su zama abin koyi a bangarori 4 na da hangen nesa sosai, kuma suna da babbar ma’ana wajen gina ingantaccen tsarin shugabancin duniya mai adalci. Wani masanin fasahar AI na kasar Jamus ya bayyana cewa, sabbin ra’ayoyi da sabbin shawarwari da shugaba Xi ya gabatar a cikin jawabinsa, tushe ne da ke ciyar da bunkasar sabbin masana’antu a duniya.
A shekarar 2027, kungiyar BRICS za ta shiga “Shekarar Sin” ta hudu. Al’ummar duniya gaba daya suna fatan bangaren Sin zai kara taka rawar gani, don ciyar da “hadin gwiwar BRICS” gaba ba tare da tangarda ba.
Daraktan cibiyar binciken yankin Asiya da tekun Pasifik na kasar Rasha, Sergey Sanakoev yana da kwarin gwiwa cewa, a shekara mai zuwa Sin za ta hada gwiwa da kasashe masu tasowa don karfafa samun karin ci gaba tsakanin kasashe mambobin BRICS bisa tushen ruhinta, don tattara karin karfi ga ci gaban kasashe masu tasowa tare. (Amina Xu)














