Yadda Ya KamataKwanan nan, tsohon firayim ministan Jordan Omar Razzaz, ya shaidawa manema labarai na CMG, cewa yanzu haka ana shiga sabon zamani na fasahar AI, da mutum-mutumin inji da fasahar dijital, kuma babu shakka wadannan fasahohi suna yin tasiri mai zurfi ga rayuwar mutane.
Ya kamata a yi amfani da irin wadannan fasahohi yadda ya kamata, kuma a ganinsa kasar Sin tana nuna himma da kwazo a wannan fannin.Yayin da aka tabo maganar matsayi da ka’idojin da kasar Sin ke rike da su kan batun gudanar da fasahar AI, Omar ya bayyana cewa, Sin ta riga ta shiga sahun gaba a duniya wajen gudanar da fasahar AI a duniya.
Fasahar AI fasaha ce mai inganci kuma ta zamani. A watan Yulin bana, shugaba Xi ya nuna cewa, “ci gaban fasahar AI bai kamata ya zama wasan kide-kide na wata kasa daya ba, a’a, ya kamata ya zama wasan kide-kide na hadin gwiwar duniya.” Kasar Sin tana fatan kasashe daban-daban su hada kai don kare muradun dan Adam da mutuncinsa, da kuma ciyar da ci gaba da wadatar dan adam gaba. (Amina Xu)














