ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, October 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Miƙa Kaina Ga Hukumomin Tsaro – Sanata Shehu Buba

by Abubakar Sulaiman
1 month ago

Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar, ya ce a shirye yake ya fuskanci cikakken bincike daga hukumomin tsaro kan zarge-zargen da ake yi masa na alaƙa da ’yan bindiga, ko ɗaukar nauyin ta’addanci ko garkuwa da mutane. Buba ya ce shi da kansa ya miƙa kansa ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Da yake magana da ’yan jarida a Bauchi ranar Litinin, Sanatan ya ce “babu abin da nake ɓoyewa, kuma babu wani abin da nake fargabar a bankaɗo a kaina.” Ya ce ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya, yana mai cewa bai taɓa ɗaukar nauyin ’yan bindiga ko tallafa musu da kuɗi, ko makamai ko wata hanya ba. Ya ce zarge-zargen sun fara ne tun shekarar 2024 a matsayin yarfen siyasa, kafin su sake bayyana ta wasu hanyoyi.

Buba ya ce tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Yakubu Chonoko Maikyau, SAN, ta rubuta wa DSS, da Hukumar Leƙen Asirin Tsaro ta Sojoji (DIA) da Rundunar ’Yandandan, inda ta nemi a gudanar da bincike kan zarge-zargen. Ya kuma ƙalubalanci duk wanda ke da hujjar alaƙarsa da ’yan bindiga, ta’addanci ko garkuwa da mutane da ya miƙa ta ga hukumomin tsaro maimakon ya yaɗa zarge-zargen a kafafen sada zumunta.

ADVERTISEMENT

Sanatan ya ce ya amince a gurfanar da shi a gaban kotu kuma a hukunta shi idan bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu a ayyukan laifin da ake zarginsa da su. Ya kuma ce hukumomin tsaro su gayyaci mutanen da ke yaɗa zarge-zargen domin su gabatar da hujjojin da suke da su. Buba ya ƙara da cewa ya taɓa jagorantar Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Leƙen Asiri, inda ya yi aiki tare da sojoji da hukumomin leƙen asiri wajen yaƙi da ’yan bindiga, ta’addanci da garkuwa da mutane.

Buba ya ce lauyoyinsa sun kuma gano wani mai suna Hassan Saleh Hussaini, wanda yake zargin yana da hannu wajen yaɗa wasu daga cikin zarge-zargen daga Jamhuriyar Nijar. Ya ce an kai rahoton lamarin domin neman taimakon Interpol, yayin da aka ɗauki lauyoyi a Nijar domin bin hanyoyin shari’a.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus

Ɗaliban Kano Sun Lashe Gasar Ƙasa Da Ƙasa Da Manhajar AI Ta Noma

Sanatan, wanda shi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar PRP a 2027, ya ce yana ganin wasu na amfani da zarge-zargen ne a matsayin yarfen siyasa domin rage masa damar samun nasara a zaɓen gwamna na 2027.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    2027: Babu Wani Ɗan Takarar Adawa Da Zai Samu Kashi 25% Na Ƙuri’un Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Bayanin Sojoji Kan Taƙaddamarsu Da Ƴansanda A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    NDC Ta Tsige Ɗan Takararta A Borno Kan Zargin Yi Wa Atiku Kamfe
  • Abubakar Sulaiman
    An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

MASU ALAKA

Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus
Labarai

Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus

October 27, 2026
Ɗaliban Kano Sun Lashe Gasar Ƙasa Da Ƙasa Da Manhajar AI Ta Noma
Labarai

Ɗaliban Kano Sun Lashe Gasar Ƙasa Da Ƙasa Da Manhajar AI Ta Noma

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Aikin Inganta Wutar Lantarki A Kano Da Katsina
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Aikin Inganta Wutar Lantarki A Kano Da Katsina

October 27, 2026
Next Post
Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

October 27, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Jihohi Uku

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Jihohi Uku

October 27, 2026
Amnesty International Da Ƙungiyar Matasan Arewa Sun Nemi A Yi Wa Sheikh Masussuka Adalci

Amnesty International Da Ƙungiyar Matasan Arewa Sun Nemi A Yi Wa Sheikh Masussuka Adalci

October 27, 2026
Gwamnan Katsina Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Sheikh Masussuka, Ya Nemi A Gudanar Da Bincike

Gwamnan Katsina Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Sheikh Masussuka, Ya Nemi A Gudanar Da Bincike

October 27, 2026
Ballon d’Or: Yamal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Matashin Ɗan Wasa Karo Karo Na Uku A Jere

Ballon d’Or: Yamal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Matashin Ɗan Wasa Karo Karo Na Uku A Jere

October 27, 2026
Kotu Ta Hana Miji Magana Da Matarsa Tsawon Mako Biyu

Kotu Ta Tsare Wani Mutum Kan Zargin Barazanar Yaɗa Hotunan Tsiraicin Gwamnan Kano

October 27, 2026
’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.