Jimilar darajar hada-hadar shige da fice ta cinikin kayayyaki ta Sin ta karu da kashi 17.3% a watanni bakwai na farkon bana bisa makamancin lokacin a bara. A ciki kuma, kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje sun karu da kashi 22%, wanda hakan ya nuna saurin karuwar adadin ta fi na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, a cikin watanni biyar a jere. Alkaluman sun yi bayanin cewa, a halin yanzu, Sin ba “babbar mai sayar da kayayyaki” ba ce kawai a duniya, ita ce kuma “babbar mai sayen kayayyaki”.
A wannan shekarar, wasu ’yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun yayata abin da ake kira “Sin tana matsin lamba”, inda suke ikirarin cewa rarar kudin Sin tana “sanya lamba” ga kasuwar duniya. Wadannan kalaman sun saba wa ka’idodin tattalin arziki da ainihin gaskiya, kuma sun fuskanci shakku daga jama’ar duniya.
Gaskiya ita ce mafi kyawun martani ga batancin da kasashen yamma ke yi wa Sin. A matsayinta na “babbar mai sayar da kayayyaki,” Sin ta ci gaba da samar wa duniya kayayyaki masu inganci da araha cikin kwanciyar hankali. Ban da haka kuma, Sin ta ci gaba da fadada bude kofarta cikin babban mataki, tana kara amfani da fa’idojinta na “babbar mai sayen kayayyaki” da kuma mayar da babbar kasuwarta zuwa babbar dama ga duniya.
Abin mafi mahimmanci shi ne, karuwar shigo da kayayyaki daga Sin ya taimaka wa kasashe da yawa masu tushen albarkatu da masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje habaka tattalin arzikinsu, wanda ya inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya mai hada kai da kawo alheri ga kowa da kowa. (Safiyah Ma)














