Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta fitar da wani sabon rahoto da ke nuna cewa farashin iskar gas na girki (LPG) ya yi mummunan tashin gwauron zabi, inda ya kai matsaya mafi tsada na (Naira 1,575 kan kowane kilogiram a Jihar Sokoto) a watan Yulin 2026. Wannan tsadar ta sanya Sokoto zama jiha mafi tsadar iskar gas a cikin manyan birane shida da hukumar ta bi diddiginsu a faɗin ƙasar.
A cewar sakamakon binciken da ke ƙunshe a cikin takardar bayanan hukumar, farashin matsakaici na gas ɗin ya bambanta daga gari zuwa gari. Jihar Legas ce ke da farashi mafi sauƙi wanda ya tsaya kan Naira 1,325 kan kowane kilogiram, wanda ke biye da ita kuma su ne [Kano da Enugu da ke sayarwa a Naira 1,550]. Har ila yau, rahoton ya nuna cewa a garin Ibadan farashin yana kan Naira 1,540, yayin da a Calabar ya kasance Naira 1,410. Bayanai sun nuna cewa a wasu lokutan, farashin yakan yi tashin gwauron zabi har zuwa Naira 1,650 a garuruwan Kano, Sokoto, da Enugu.
Wannan tashin farashin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun karuwar yawan gas ɗin da ake samarwa a cikin gida. NMDPRA ta bayyana cewa yawan iskar gas da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4% cikin ɗari, inda ya tashi daga kiloton 5.1 a kowace rana a watan Yuni, zuwa kiloton 5.3 a watan Yuli.
Hukumar ta nuna cewa ƙaruwar ta faru ne sakamakon cewa rukunin da ake samarwa a cikin gida ya tashi da kashi 22%, alhali kuwa [shigo da shi daga ƙasashen waje ya ragu da kashi 40%]. Kamfanonin NLNG ne suka fi kawo gas din da ya kai kiloton 2.031, yayin da sauran masana’antu da matatar Dangote suka biyo baya.
Koda yake an samu ƙarin adadin abin da ake samarwa, amma [hawan farashin na nuni da cewa yawan masu saye shima ya ƙaru da kashi 7%] inda hakan ke takaita adadin gas din da ke jiran masu saye. Hukumar ta kuma tabbatar da cewa, a halin yanzu, adadin iskar gas ɗin da ake da shi zai iya kai kwanaki 16.3 kacal, wanda ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da mizanin kwanaki 30 da ake buƙata.














