Mutane 15 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya faru ranar Lahadi a kan titin Kano zuwa Zariya, a yankin Gadar Yankifi da ke Jihar Kano.
Hatsarin ya rutsa da wata tirela ƙirar DAF da ke ɗauke da fasinjoji da kayayyaki.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta ce motar ta yi hatsari ita kaɗai da misalin ƙarfe 5 na Asuba.
Jami’an FRSC sun isa wurin da hatsarin ya faru cikin mintuna biyar tare da ceto dukkanin mutane 15 da suka jikkata.
Daga bisani, an kai su Babban Asibitin Kura domin samun kulawar likitoci.
Ba a samu asarar rai ba a hatsarin.
Hatsarin ya dan toshe hanyar Kano zuwa Zariya na wani lokaci, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa.
Daga bisani, jami’an FRSC sun ɗauke motar daga kan hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa.
Hukumar FRSC ta buƙaci masu ababen hawa da su riƙa tuƙi cikin kulawa, su rage gudu tare da bin dokokin hanya.














