Farashin man fetur ya ƙaru zuwa naira 1,370 kan kowace lita a Jihar Legas, sakamakon sabon ƙarin da aka samu a farashin fetur a gidajen mai.
Binciken da aka gudanar ranar Talata ya nuna cewa gidajen mai na MRS da NNPC suna sayar da fetur kan kowa lita a naira 1,360, yayin da Mobil ke sayarwa kan naira 1,349.
Wasu ’yan kasuwa kuma suna sayar da litar tsakanin naira 1,365 zuwa naira 1,370.
Wasu manyan gidajen man fetur, ciki har da A.A. Rano, NIPCO, African Terminal da Aiteo, sun ƙara farashin man fetur.
An kuma samu ƙarin farashi a Fatakwal da Warri, yayin da a Calabar farashin litar man fetur ya kai naira 1,360.
A wani ɓangare kuma, farashin dizal ya sauka a wasu gidajen mai da ke Legas da Warri, yayin da wasu suka bar farashinsu yadda yake.
Wannan sabon ƙarin ya nuna yadda farashin man fetur ke ci gaba da sauyawa a sassan ƙasar.














