Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar-Faruk, ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta kafa dokar da za ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.
Sarkin ya yi wannan kiran ne ranar Talata yayin wani taron wayar da kan jama’a da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta shirya a Daura, Jihar Katsina.
Ya buƙaci ’yan majalisa su ƙarfafa dokokin da ake da su tare da samar da hukunci mai tsauri domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da shan su.
Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta tallafa wa duk wani shiri na yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa wannan yaƙi na da matuƙar muhimmanci ga makomar Arewacin Nijeriya da ƙasa baki ɗaya.
Tun da farko, jami’an NOA sun bayyana cewa sun zaɓi Jihar Katsina domin gudanar da taron ne saboda yawan matsalolin da suka shafi miyagun ƙwayoyi a yankin Arewa maso Yamma.
Sun buƙaci al’umma, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta hanyar wayar da kan jama’a da ɗaukar matakan haɗin gwiwa.














