Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗora alhakin rashin nasarar ’yan jam’iyyar Republican a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki kan yaƙin da ake yi da Iran, yayin da jam’iyyar Democrat ta samu gagarumar nasara a faɗin ƙasar.
Trump ya ce masu zaɓe sun goyi bayan matsayinsa kan Iran, amma ba su ji daɗin tashin farashin man fetur da yaƙin ya haddasa ba.
Ya taya ’yan Democrat murnar nasarar da suka samu, tare da cewa a shirye yake ya yi aiki da su duk da cewa sun karɓe ikon Majalisar ƙasar.
’Yan Democrat sun samu nasara a wasu jihohin da a baya ake ganin na goyon bayan Republican ne, ciki har da Kansas, Iowa, Texas, South Carolina, North Carolina da Ohio.
Sun kuma karɓe ragamar Majalisar Dattawa da ta Wakilai, lamarin da ya kawo ƙarshen rinjayen Republican a Majalisar Dokokin Amurka.
Trump ya yi gargaɗin cewa zai yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen ƙin amincewa da duk wani ƙuduri da bai goyi bayansa ba.
Masu sharhi sun danganta nasarar Democrat da damuwar al’umma kan matsin tattalin arziƙi, cin hanci da rashawa da kuma yaƙin Iran.














