ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

by Sadiq
57 minutes ago

Jam’iyyar ADC ta ɓoye wajen da za ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Jihar Sakkwato saboda fargabar yiwuwar kawo cikas ga taron.

An shirya fara gangamin ne a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026, a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin jam’iyyar da Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Dahiru Maishanu, ya ce jam’iyyar ta samu wajen gudanar da taron, amma tana jiran amincewar hedikwatarta ta ƙasa kafin bayyana wajen.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta tuntuɓi ’yansanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kan rahotannin shirin kawo cikas ga taron.

Ya ce hukumomin sun yi alƙawarin samar da isasshen tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Sanata Sahabi Kaura Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC A Zamfara Ta Arewa

Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya zargi DSS da Gwamnatin Jihar Sakkwato da ƙoƙarin kawo cikas ga gangamin.

Ya yi zargin cewa ana haɗa wasu masu zanga-zanga ne domin haddasa tarzoma, lamarin da ka iya bai wa gwamnati damar sanya dokar hana fita.

Sai dai DSS ta musanta zargin, amma ta ce Darakta Janar na hukumar ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kare matakin rufe ofishin ADC, inda ta ce hakan ya zama dole domin hana sake ɓarkewar rikici bayan arangama tsakanin magoya bayan ADC da PDP.

Sai dai ADC ta dage cewa za ta gudanar da gangamin kamar yadda aka tsara, tare da gargaɗin gwamnati kan katsalandan a harkokin siyasar jam’iyyar.

MASU ALAKA

Sanata Sahabi Kaura Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC A Zamfara Ta Arewa
Siyasa

Sanata Sahabi Kaura Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC A Zamfara Ta Arewa

November 3, 2026
Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello
Siyasa

Mako Biyu Zan Yi A Kano Don Tabbatar Da Nasarar Tinubu – Yahaya Bello

November 1, 2026
ADC Ta Yi Gargaɗi Kan Rikicin Siyasa Bayan Harin Da Aka Kai Wa Ɗan Takararta A Sakkwato
Siyasa

ADC Ta Yi Gargaɗi Kan Rikicin Siyasa Bayan Harin Da Aka Kai Wa Ɗan Takararta A Sakkwato

November 1, 2026
Next Post
Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran

Trump Ya Ɗora Alhakin Shan Kayen Da Jam’iyyarsa Ta Yi Kan Yaƙin Iran Yayin Da Democrat Ta Yi Nasara

LABARAI MASU NASABA

Trump Ya Yi Barazanar Ƙaƙaba Haraji Kan Ƙasashen Da Ke Kasuwanci Da Iran

Trump Ya Ɗora Alhakin Shan Kayen Da Jam’iyyarsa Ta Yi Kan Yaƙin Iran Yayin Da Democrat Ta Yi Nasara

November 4, 2026
ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

November 4, 2026
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Bashin Da Ake Ci Na Barazana Ga Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sanusi II

November 4, 2026
Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

November 4, 2026
Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

November 3, 2026
Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

November 3, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

November 3, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Za Mu Biya Ma’aikata Alawus ɗin Sufuri na Naira 70,000 — Gwamnatin Kebbi

November 3, 2026
Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

November 3, 2026
Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin

Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin

November 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.