ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fatan Sassan Kasa Da Kasa Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Amurka

Manazarta da dama na bayyana cewa cikin shekaru kusan 10 na baya bayan nan, alakar kasashen Sin da Amurka ta fuskanci manyan sauye-sauye, ciki har da sauyin da aka gani a farkon shekarar 2018, lokacin da Amurka ta bullo da manufar kakabawa hajojin Sin da ake shigarwa Amurka harajin fito. Bayan hakan, an samu daidaiton yanayi bayan gudanar da jerin shawarwari, da tuntubar juna a matakai daban daban.

Baya ga shekarar 2018, a shekarar 2025 da ta gabata ma alakar Sin da Amurka ta ci karo da wani sabon zagaye na tirka-tirka, kafin kaiwa ga cimma daidaito da ya biyo bayan jerin tarukan tuntuba tsakanin shugabannin kasashen biyu da kuma tawagogin wakilansu.

Tabbas babu wani mataki da zai iya warware sabani, da rashin fahimtar juna tsakanin wadannan manyan kasashe dake kan gaba a karfin tattalin arziki a duniya, illa ci gaba da tattaunawa, da martaba matsayar da suka cimma yadda ya kamata.

ADVERTISEMENT

A lokuta mabambanta, kasar Sin ta jure sauye-sauyen yanayi a dangantakarta da Amurka, wanda hakan ya haifar mata da karin martaba tsakanin sassan kasa da kasa, tare da samar da yanayi mai kyau na warware bambance-bambancensu ta hanyar aiwatar da shawarwari.

A yau, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, ya furta fatan gudanar da babbar tattaunawa tare da shugaba Xi. Yana mai cewa akwai yiwuwar cimma babban sakamako tsakaninsu.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Ko shakka babu ganawar manyan shugabannin biyu a wannan karo, ta zo a gabar da suke kara amincewa da muhimmancin daidaito, da martaba juna, da burin cimma moriyar bai daya, wanda hakan ya dace da muradun daukacin sassan kasa da kasa.

Fatan dukkanin sassan kasa da kasa a wannan gaba shi ne kari kan yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a baya, da sakamakon tuntubar da jami’an kasashen biyu suka sha, ganawar shugaba Xi da shugaba Trump ta wannan karo za ta yi armashi, kuma za a kai ga cimma matsaya kan muhimman batutuwan da kasashen biyu ke mayar da hankali a kansu.

Kazalika, duniya na begen ganin Sin da Amurka sun rungumi juna, tare da zakulo hanyoyin daga matsayin dangantaka bisa manyan tsare-tsare, da ingiza ci gaban alakarsu cikin tsari, da martaba juna, da zaman jituwa, da hadin gwiwar cimma moriyar bai daya, ta yadda hakan zai amfane su tare da sauran sassan duniya baki daya.

Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
Amurka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnati Ta Jibge Jami’an Tsaro Domin Gudanar da Zaɓen Fidda Gwanin APC A Nasarawa

Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kamfanin Haƙar Ma’adanai Saboda Rikicin Shari’a

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.