ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kamfanin Haƙar Ma’adanai Saboda Rikicin Shari’a

by Zubairu M Lawal and Sulaiman
4 months ago
Nasarawa

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta rufe kamfanin haƙar ma’adanai na Lideal Mines Company da ke aiki a yankin ci gaban raya Kasa dake Udege, a ƙaramar hukumar Nasarawa, sakamakon wani rikicin shari’a da ya daɗe yana gudana tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin.

Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dakta Margaret Elayo, ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

Dakta Elayo ta bayyana cewa bayan jerin tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da nazarin rahotannin tsaro da suka shafi ayyukan haƙar ma’adanai a yankunan da abin ya shafa, gwamnatin jihar ta umarci kamfanin da ya fara janye dukkan kayayyakin aikinsa daga wurin nan take.

ADVERTISEMENT

A cewarta, umarnin ya haɗa da cire injinan haƙar ma’adanai, manyan motoci, sauran kayan aiki da kuma ma’aikatan kamfanin daga wurin haƙar ma’adanan.

Ta ce matakin ya yi daidai da ƙudirin Gwamna Abdullahi Sule na tabbatar da halastattun ayyukan haƙar ma’adanai, kiyaye zaman lafiya a yankunan ma’adinai da kuma tabbatar da bin umarnin gwamnati da ƙa’idojin aiki da aka gindaya a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Kwamishinar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta bai wa kamfanin wa’adin da zai cika domin bin umarnin gaba ɗaya.

Ta ce:“Umarnin ya kuma tanadi dakatar da duk wani nau’i na ayyukan haƙar ma’adanai da kuma fitar da albarkatun ƙasa daga wurin cikin wa’adin da aka bayar.“

Gwamnati ta bayyana a sarari cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kare muradun jama’a da kuma ci gaba da ƙoƙarin sake tsara fannin haƙar ma’adanai a Jihar Nasarawa ta yadda za a samu saka hannun jari mai inganci, ƙara darajar albarkatun ƙasa a cikin gida, da haɗin kan al’umma da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

“Gwamnan ya sha nanata cewa duk ayyukan haƙar ma’adanai a jihar dole ne su dace da manufofin gwamnati, musamman buƙatar masu saka hannun jari su kafa ingantattun cibiyoyin sarrafa ma’adanai da za su amfani al’ummomin da ke yankunan da ake haƙar ma’adanan tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga tattalin arzikin jihar.”

Dakta Elayo ta ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta tura jami’an tsaro zuwa wurin haƙar ma’adanan domin tabbatar da cikakken bin umarnin da aka bayar.

Ta kuma jaddada cewa gwamnatin Jihar Nasarawa na ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayi mai kyau ga sahihan masu saka hannun jari da ke shirye su bi dokoki, manufofi da muradun ci gaban jihar.

Nasarawa
Zubairu M Lawal
+ posts Bio
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    2027: Miyetti Allah Ta Yi Barazanar Ƙauracewa APC Kan Ci Gaba da Tsare Boɗejo
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Samar Da Abinci Mai Gina Jiki: Gwamna Sule Ya Duba Gonakin Shinkafa A Jangwa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda Ya Tallafawa Manoma Da Kayan Aikin Gona Na Miliyoyin Naira A Nasarawa
Nasarawa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Shugaba Xi Ya Gana Da ‘Yan Kasuwan Amurka Da Suka Rako Shugaban Amurka

Shugaba Xi Ya Gana Da 'Yan Kasuwan Amurka Da Suka Rako Shugaban Amurka

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.