Aƙalla fursunoni shida ne aka bayar da rahoton cewa sun mutu sakamakon zargin ɓarkewar cutar kwalara a wani gidan gyaran hali da ke Jihar Kano.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International ce ta bayyana hakan, inda ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda cutar ke shafar ɗaurarru tare da yin kiran gaggawa ga mahukunta domin ɗaukar matakan ceton rayuka.
A cewar ƙungiyar, matsalar cunkoson da ya addabi gidan gyaran halin, rashin tsaftataccen ruwan sha, da kuma ƙarancin kayan aiki a sashin lafiya na daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da wannan mummunan hali tare da ba wa cutar damar yaɗuwa cikin sauri.
Rahoton KanoTimes ya bayyana cewa, Amnesty ta buƙaci Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) da Ma’aikatar Cikin Gida da su gaggauta kai agajin magunguna, da samar da wadataccen ruwa mai tsafta, da killace waɗanda suka kamu, da kuma gudanar da bincike na gaskiya kan mutuwar fursunonin.
A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada buƙatar rage cunkoso a gidajen gyaran halin Nijeriya baki ɗaya, tare da tabbatar da an mutunta haƙƙin fursunoni na samun ingantaccen yanayin rayuwa da cikakkiyar kulawar lafiya kamar yadda dokokin ƙasa da na ƙasa da ƙasa suka tanada.














