Sojojin Nijeriya sun samu nasarar tare mutane 43 waɗanda suka iyalai ga mayaƙan ƙungiyar ISWAP, tare da ceto wasu mutum tara da aka yi garkuwa da su a yayin sumamen da suka kai a Arewa Maso Gabas.
A cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar, dakarun sun samu wannan nasara ne bayan gudanar da sintiri da ayyukan share maɓoyar ƴan ta’adda, lamarin da ya tilasta wa mayaƙan tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rahoton ya bayyana cewa mambobin iyalan mayaƙan na ISWAP guda 43, waɗanda mafi yawansu mata ne da ƙananan yara, an tare su ne yayin da suke ƙoƙarin tserewa sakamakon matsin lambar hare-haren da rundunar sojin ke kaiwa a sansanoninsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an tura mutum tara da aka kuɓutar zuwa cibiyar lafiya domin duba lafiyarsu kafin a miƙa su ga iyalansu, yayin da ake ci gaba da tantance iyalan mayaƙan domin ɗaukar matakan da suka dace na tsaro da jin ƙai.
A ƙarshe, rundunar sojin ta jaddada ƙudurinta na ci gaba da kai hare-hare domin kakkaɓe ragowar ƴan ta’adda a yankin baki ɗaya, tana mai buƙatar al’umma da su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai.














