Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya kammala bita ta karshe ta tsarin tufafin ado na bikin bazara na shekarar 2026, wanda za a watsa da misalin karfe 8 na dare a ranar 16 ga Fabarairun nan. Jerin bitocin da aka yi guda biyar sun kara kawata mabambantan shagulgulan da aka shirya yi da suka kunshi kide-kide, raye-raye, zane-zanen barkwanci, sihiri, da kuma sassan al’adu a babban dandamalin bikin da kuma sauran ressansa na yankuna hudu.
Wannan dabdala ta shekara-shekara za ta raka masu kallo a duk fadin duniya wajen shiga sabuwar shekarar Doki ta gargajiyar Sinawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

Discussion about this post