ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi: Ya kamata A Inganta Harkokin Jagorancin Duniya Ta Hanyar Yin Gyare-gyare 

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Wang

Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a ranar Asabar da ta gabata cewa, ya kamata a kyautata tsarin jagorancin duniya ta hanyar yin gyare-gyare domin daidaita tsarin tarihi.

Wang, mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a zaman taron da aka yi mai lakabin “Sin a duniya” a babban taron tsaro na Munich da ke gudana.

Wang ya ce, al’amuran kasa da kasa sun kara shiga garari da kwan-gaba-kwan-baya a cikin shekarar da ta gabata. Amfani da irin tsarin rayuwar namun daji da yin gaban-kai sun kara yawaita, kuma dalilin zaman lafiya da ci gaban dan Adam sun hau kan wani sabon siradi.

ADVERTISEMENT

Wang ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya, inda ya yi kira da a aiwatar da daidaiton ‘yancin mallakar kasa, da bin dokokin kasa da kasa, da tsarin mabambantan bangarori, da amfani da tsari mai fifita al’umma, da aiwatar da matakai na hakika, a kokarin da ake yi na gina tsarin jagorancin duniya mafi adalci da kuma cancanta.

Wang ya yi kira da a yi kokarin cimma tsagaita bude wuta da sake gina Gaza, yana mai cewa aiwatar da shawarar kafa kasashe biyu, da maido da yin gaskiya da adalci ga al’ummar Falasdinu, wani nauyi ne da al’ummomin kasashen duniya ba za su iya guje masa ba. Sannan, halin da ake ciki a Iran ya shafi yanayin zaman lafiya gaba daya a yankin gabas ta tsakiya, don haka ya kamata dukkan bangarorin da abin ya shafa su yi taka-tsan-tsan don kauce wa haddasa sabuwar fitina.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Kazalika, bisa yadda rikicin Ukraine ya bude kofar tattaunawa, Wang ya ce, kamata ya yi dukkan bangarorin da abin ya shafa su yi amfani da wannan damar wajen kokarin cimma daidaito, da yarjejeniya mai dorewa, da kashe wutar musabbabin tashe-tashen hankula, da samar da zaman lumana na dogon lokaci a yankin Turai. Game da batun Venezuela kuma, bai kamata a ketare bin dokokin kasa da kasa ba, kuma dole ne a kiyaye ka’idar ‘yancin mallakar kasa.

Wang ya ce, kasar Sin za ta kasance mai ba da gudummawa sosai wajen samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban tarihi, kuma za ta sa kaimi ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Wang
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Wang
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Za A Wallafa Makalar Shugaba Xi Kan Muhimman Ayyukan Da Ke Kunshe A Aikin Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Yanzu

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci