Jama’a barkanku da juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, dana nesa. A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gaishe-gaishen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkanin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman edita na Abdulrazak Yahuza Jere, da sauran al’ummar musulmi baki daya, da fatan an yi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka:
Assalamu alaikun. Fatan alkairi ga LEADERSHIP Hausa , ina mai farin cikin da wannan fali namu da aka bamu dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya daukaki wannan Jarida mai farin jini a Duniya baki daya. Ina so in mika sakon gaisuwar Joron Juma’a ga, manyan abokan karatuna kamar su Tasi’u Sirajo (Barrister), da Yunus Abubakar, tare da Rabi’u Abdullahi (baban Tahir), sai kuma Haruna Ibrahim (Baba), da Zakariyya Umar Wade, daga karshe ina mika sakon gaisuwar Goron Juma’a ga Aliyu Muhammad. Da fatan duk suna nan cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a.
Daga Abdulmuminu Sani, Katsina.
08135391867
Dubu gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokanaina kamar haka Muhammad Idris, sai kuma Kalifa baba Ahmad, tare da Umar Dogara Inkiya Lauka-lauka,da Adon Wanki wato baban Amir da Muhibbat, Oga Ubale Mai wanki da guga, tare da Zubairu Dogi, daga karshe ina mai mika gaisuwar Goron Juma’a ga Dan ladi Kalmi. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin.
Daga Abdullahi Mai Kano, Kaduna.
08026441039
Salam, LEADERSHIP A YAU Juma’a ina so ku bani dama in mika gaisuwar Goron Juma’a ga abokanaina kamar su Alhaji Sadiku Umar Faki, sai kuma Ibrahim Sakatare Malikanci Ikara, tare da Musa Digaga, da Baba Iyabo Dan Danga, sai Magaji gurgu mai said a yalo, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga kanina Arrama mai sai yalo mile 12 Legas. Da fatan duk suna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka amin.
Daga Jinjiri Mile 12, Legas.
09023489162
Da farko, ina mika sakon Goron Juma’a ga abokaina Muhammad Danladi, sai kuma Muhammad Idris mai shago a Lake Biew Homes Phase 2, Abuja, da Mahmud Abubakar, tare da Abubakar Isa Manaja, da kuma Yahya Haruna, da Surajo Aliyu, daga karshe ina mika sakon Goron Juma’a ga Bello Inuwa. Da fatan duk suna nan cikin.