Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya rushe Hukumar Gudanarwar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi (KEBSIEC).
An bayyana hakan ne cikin wata wasika da Daraktan Majalisar Zartarwa, Kabiru Hassan Wasagu, ya fitar, wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da rushe hukumar ne bayan wa’adin da aka ba mambobinta ya ƙare, inda matakin ya fara aiki daga 18 ga Satumba, 2026.
Sai dai gwamnati ta bayyana cewa sauran mambobi biyu na hukumar waɗanda wa’adinsu bai ƙare ba za su ci gaba da kasancewa a kan muƙamansu har sai an sake kaddamar da wasu jagororin hukumar.
Gwamna Idris ya yabawa mambobin da wa’adinsu ya ƙare bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen yi wa jihar hidima.
Ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatinsa ta ƙara kare ’yancin kai da amincin hukumar zabe domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci a jihar.














