ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 hours ago
Afirka

Kasashe 164 sun jefa kuri’ar nuna amincewa, a yayin da Amurka kadai ta ki, kuma da haka ne Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da wani kuduri a kwanakin baya, wanda ke karfafa gwiwar kasa da kasa su yi watsi da taswirar duniya ta tsarin Mercator da aka yi amfani da ita sama da shekaru 450, su kuma yi amfani da sabuwar taswira mai tsarin “Equal Earth” da aka samar a shekarar 2018.

Kasar Togo ce ta gabatar da shawarar kada kuri’a ga shirin kudurin, wadda ta samu goyon baya daga Kungiyar Tarayyar Afirka. Dalilin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta karfafa gwiwar kasa da kasa wajen fara amfani da taswira mai tsarin “Equal Earth”, ba saboda takaddamar filayen kasa ba ne, sai dai saboda kuskuren da ake samu a taswirar da ake amfani da su a yanzu, wato mai tsarin Mercator, wadda masanin taswira dan kasar Netherlands mai suna Mercator ya kirkira a shekarar 1569, a kokarin magance matsalolin da aka fuskanta wajen jagorantar zirga-zirgar jiragen ruwa, sai dai wannan tsarin taswira ya haifar da rashin gaskiyar fadin filaye, wato kasashen da suke nesa da ikwaitar duniya, an kara girmansu a taswirar, don haka, in mun duba taswirar, fadin nahiyar Afirka tamkar ya yi daidai da na tsibirin Greenland, amma hakikanin gaskiyar ita ce fadin Afirka ya ninka na Greenland har sau 14.

Ga kasashen Afirka, wannan ba batun fasahar zana taswira ba ne, a’a, a maimakon haka, batu ne na gyara bahaguwar fahimtar nahiyar ta tsawon sama da shekaru 450. Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey, a jawabin da ya gabatar a taron Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “Taswira mai adalci ba za ta canza yanayin yankunan duniya ba, abin da za ta canza shi ne yadda muke kallon duniya.” Cikin sama da shekaru 450 da suka wuce, yaran duniya baki daya, har da na Afirka, taswirar da ta rage girman Afirka suke gani a makarantu. Kungiyar Tarayyar Afirka ita ma ta nuna cewa sama da shekaru 450, duniya tana fahimtar Afirka a kan “taswirar da ba daidai ba.”

ADVERTISEMENT

A matsayinta na kasa daya tilo da ta kada kuri’ar kin amincewa, Amurka ta bayyana cewa, wannan kudurin yana da ma’anar siyasa mai zurfi a bayansa, yayin da rahoton kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya yi nuni cewa, taswirar mai tsarin “Equal Earth” ta rage girman Amurka da Turai a taswirar, kuma hakan ya jawo rashin jin dadin Amurka. Lallai, ita Amurka ta ki amincewa da sauya taswirar ne domin ta riga ta saba da wannan girman da aka kara mata.

Abin farin ciki shi ne, yawancin kasashen duniya sun goyi bayan Afirka. Faransa a ranar kada kuri’ar ta sanar da cewa za ta yi watsi da amfani da taswira mai tsarin Mercator.

LABARAI MASU NASABA

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

Ministan harkokin wajen kasar, Jean-Noël Barrot ya ce: “Canza taswirar da ake amfani da ita ba zai iya canza duniya ba, sai dai hakan zai gyara hanyar nunawa da ba ta dace ba, wanda shi kansa aiki ne na kiyaye gaskiya.”

A lokacin da Togo ke jawabi a madadin kasashen Afirka a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kuma a lokacin da kasashe 164 suka amsa kiran “gyara bahaguwar fahimta” da kuri’un nuna amincewa, wannan ba sauyin fasahar zana taswira ba, maimakon haka canji ne mai zurfi da ke faruwa ga tsarin duniya, wato kasashe masu tasowa ba za su zama ’yan kallo masu shiru ba, kuma kasashen Turai ma ba za su ci gaba da bin jagorancin Amurka ba, kuma duniya na sabawa da yanke shawara ba tare da amincewar Amurka ba.

Daga shekarar 1569 zuwa 2026, daga karshe an kai ga gyara wannan kuskuren nuni a taswira. Fadin Afirka bai taba canzawa ba, abin da ya canza shi ne yadda duniya ke kallonta. A yayin da yaran Afirka a taswira suke ganin girman da ya dace na nahiyarsu, ba wai kawai fahimta madaidaiciya suka samu ba, har ma da wani matsayi mai adalci, wato Afirka ta ki a sake “rage” girmanta, sabo da ita kanta nahiya ce mai fadi, wadda har ta kai ga za ta iya daukar nauyin makomarta, kuma ta kai ga duniya ba za ta iya kyale ta ba.

Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • Sulaiman
    Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

MASU ALAKA

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Yadda Afirka Ke Rungumar Amfani Da Damar Da Sin Ke Samarwa
Ra'ayi Riga

Yadda Afirka Ke Rungumar Amfani Da Damar Da Sin Ke Samarwa

August 28, 2026
Next Post
Ballon D'or

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin 'Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026
Ballon D'or

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.