Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kafa ƙarin sansanonin sojoji tare da tura jami’an tsaron gandun daji zuwa ƙananan hukumomin da ake fama da matsalolin tsaro.
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Muhammed Tajo Othman, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan wata ganawa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawar da Gwamna Yusuf ya yi da Ministan Tsaro kan yadda za a ƙarfafa tsaron al’ummomin da ke fuskantar barazana.
A cewar kwamishinan, sabon tsarin tsaron zai ƙara wa matakan da ake da su ƙarfi, musamman ayyukan Rundunar ’Yansanda ta Nijeriya da ‘Neighbourhood Watch’, domin inganta saurin kai ɗauki yayin fuskantar barazanar tsaro.
Gwamnatin ta ce manufar matakin ita ce ƙara kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da dakile hare-haren miyagun ƙungiyoyi a yankunan da ke cikin haɗari.














