Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da firaministan Birtaniya Andy Burnham a yau Talata. Yayin zantawar tasu, shugaba Xi ya taya Andy Burnham murnar kama aiki a matsayin firaminista. Ya ce, Sin da Birtaniya muhimman kawaye ne dake da cikakkiyar hulda bisa manyan tsare-tsare.
Kazalika, shugaba Xi ya ce duk da bambance-bambance a tsarin zamantakewa da yanayin kasashen, sassan biyu na da tarin moriyar bai daya, da suka hada su sama da bambancin dake tsakaninsu.
Daga nan sai ya yi kira ga sassan biyu, da su yi aiki tare sama da sabinin dake tsakaninsu, su nemi matsayar bai daya yayin da suke lura da bambancinsu, su kuma fadada hadin gwiwar cimma moriyar juna.
A nasa bangare kuwa, mista Burnham cewa ya yi, Birtaniya za ta wanzar da manufofinta dangane da Sin, kana za ta tsaya tsayin daka wajen gina kawance bisa manyan tsare-tsare na dogon lokaci, da daidaito tsakaninta da Sin.
Bugu da kari, Birtaniya a shirye take ta wanzar da musaya bisa matsayin koli tare da bangaren Sin, da ingiza hadin gwiwa a dukkanin bangarori, da bunkasa musayar jama’a da al’adu, da mayar da alakarsu kan turbar koli a tarihi, da haifarwa al’ummun sassan biyu tarin gajiya. Kazalika, a cewarsa matsayar Birtaniya dangane da batun Taiwan ba za ta sauya ba. (Saminu Alhassan)














