ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Halarci Taron Farko Na Liyafar Ƙungiyar ‘Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa

by Sulaiman
2 months ago

Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya halarci taron cin abincin dare na farko da Ƙungiyar ‘Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa ta shirya, wanda aka gudanar a daren Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A yayin taron, Gwamna Dauda Lawal ya samu damar sanya wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lambar girmamawa ta Babban Majiɓincin Ƙungiyar ‘Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa, wato Grand Patron of the State House Press Corps.

An shirya taron ne domin ƙarfafa alaƙa tsakanin ‘yan jarida da manyan jami’an gwamnati, karrama waɗanda suka yi fice wajen bayar da rahotannin da suka shafi Shugaban Ƙasa, tare da samar da wata dama ta tattaunawa tsakanin kafafen yaɗa labarai da manyan shugabannin gwamnati cikin yanayi na sada zumunci.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ‘yan jarida su ci gaba da riƙon ƙwarewa, gaskiya, da ɗaukar nauyin abin da suke wallafawa.

Ya bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin muhimmin abokan hulɗa wajen gina ƙasa da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Shugaban ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta kare ‘yancin aikin jarida da kuma ‘yancin faɗar albarkacin baki kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.

Ƙungiyar ‘Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙunshi ‘yan jaridar da aka ba izinin yaɗa labaran Shugaban Ƙasa da dukkan ayyukan da ake gudanarwa a cikin Fadar Shugaban Ƙasa.

Taron na farko ya samu halartar Uwargidan Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; da Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Ministan Kuɗi, Ministan Ilimi, Ministan Lafiya, Ministan Noma, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, da kuma Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Mutane 600 Ne Kacal Suka Ci Jarabawar Ɗaukar Malaman Firamare Daga Cikin 8,000

Mutane 600 Ne Kacal Suka Ci Jarabawar Ɗaukar Malaman Firamare Daga Cikin 8,000

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.