Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sakin Naira biliyan 4 domin aiwatar da kashi na biyu na Shirin Ci Gaban Al’umm, inda kowace daga cikin gundumomi 361 na jihar za ta karɓi Naira miliyan 10 domin gudanar da ayyukan da al’ummar yankin suka zaɓa bisa ga buƙatunsu.
Acikin sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ranar Laraba, 5 ga watan Agustan, ta bayyana cewa, an amince da hakan ne a taro na 12 na Majalisar Zartarwar Jihar Katsina na shekarar 2026, wanda aka gudanar a ranar Laraba a Gidan Gwamnatin Jihar. Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Dakta Bala Salisu Zango, ya ce majalisar ta kuma amince da bayar da kuɗin tallafin haɗin gwiwa na shekarar 2026 domin aiwatar da Shirin ‘Nigeria for Women Project’, wanda ke da nufin bunƙasa tattalin arziƙin mata, ƙarfafa shigar su cikin harkokin kuɗi da inganta rayuwar iyalansu.
Majalisar ta kuma amince da bayar da kwangilar samar da kayayyakin fasahar sadarwa na zamani a sabbin Makarantun Sakandaren Misali da ke Jikamshi da Dumurkul. Aikin zai haɗa da azuzuwan zamani, allunan koyarwa na dijital da cibiyar sadarwa ta zamani domin inganta koyarwa da koyo.
Haka kuma, majalisar ta amince da wallafa rahoton ci gaban Shirin Gyaran Yanayin Kasuwanci na 2025 (BERAP), a ƙarƙashin Shirin SABER, domin ƙara inganta sauƙaƙe harkokin kasuwanci, ƙarfafa gyare-gyaren gwamnati da jawo masu zuba jari zuwa jihar.
A ɓangaren samar da ruwa, majalisar ta amince da sayo sinadaran tace ruwa na kashi na biyu na shekarar 2026 tare da tura motocin dakon ruwa domin ci gaba da samar wa mazauna birnin Katsina ruwa yayin da ake gudanar da aikin gyara da inganta cibiyar samar da ruwan jihar.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa waɗannan kudurori da aka amince da su, sun nuna ƙudirin Gwamna Radda na ci gaba da bunƙasa al’ummomi, ƙarfafa tattalin arziƙin mata, inganta ilimi, aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziƙi da kuma tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar Katsina.














