Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta yi tsokaci game da labarin da ke cewa, Amurka na tsara ka’idojin hana shigar da sabbin na’urorin aika bayanai na optical transceiver modules na kasar Sin cikin Amurka.
Kakakin ma’aikatar Lin Jian ya bayyana a yau cewa, kasar Sin na adawa da yadda Amurka ke amfani da batun tsaron kasa a dukkan bangarori da kokarin dankwafe kamfanoninta ba gaira ba dalili ta hanyar amfani da karfinta.
Ya ce Sin za ta ci gaba da tabbatar da kare halaltattun hakkoki da muradun kamfanoninta.
Bayan haka, game da takardar bayani kan tsaro da Japan ta fitar a baya bayan nan, Lin Jian ya ce kasar Sin na bukatar Japan ta yi nazari mai zurfi kan laifuffuka da ta aikata a tarihi kuma ta dauki darasi daga abubuwan da suka faru a tarihi, ta daina neman dalilin fadada sojinta, kana ta dakata da ci gaba da bin turbar kuskure. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














