Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya jinjina wa gwamnatin Saudiyya bisa yi wa masu cututtukan mafitsara da hanyoyin fitsari 52 tiyata kyauta a jihar.
Ƙwararrun likitocin Saudiyya ne suka gudanar da aikin tiyatar na tsawon kwanaki shida a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), tare da tallafin gwamnatin Saudiyya da Cibiyar King Salman Humanitarian Aid and Relief.
Gwamna Yusuf ya gode wa gwamnatin Saudiyya bisa taimaka wa mutanen da ba su da halin biyan kuɗin yi wa kansu magani.
Ya ce wannan shi ne karo na huɗu da tawagar likitocin Saudiyya ta gudanar da irin wannan aikin a Kano.
Ya kuma bayyana cewa ana shirin fara tiyatar zuciya a Kano ta hanyar haɗin gwiwa da Saudiyya.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta asibitoci da faɗaɗa ayyukan lafiya na musamman a jihar.














