ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Radda Da Masari: Manyan Jami’an Gwamnatin Katsina Sun Fara Murabus Daga Muƙamansu

by El-Zaharadeen Umar
2 weeks ago

Rikicin siyasa tsakanin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da Alhaji Kabir Ibrahim Masari, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa, na ci gaba da haifar da cece-kuce a jihar, yayin da wasu manyan jami’an gwamnati suka fara murabus daga muƙamansu.

Wannan lamari ya haifar da tambayoyi daga wasu mazauna jihar kan abin da ke faruwa a gwamnatin Radda, musamman ganin cewa gwamnati ta sha bayyana cewa tana mai da hankali kan aiwatar da ayyukan da ta yi alƙawari, maimakon ɗaukar sabbin alƙawura lokacin kamfen.

ADVERTISEMENT

Sai dai a baya-bayan nan, wasu jami’an da aka ɗauka aiki a gwamnatin sun fara ajiye muƙamansu.

Wasu daga cikinsu sun bayyana komawarsu ɓangaren Ibrahim Masari, yayin da wasu ba su bayyana dalilinsu na yin murabus ba.

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

Rikicin Radda Da Masari

Rikicin tsakanin ɓangarorin biyu ya ƙara bayyana bayan zuwan Ibrahim Masari Katsina domin gudanar da harkokin siyasa da neman goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Masari da magoya bayansa na ci gaba da neman goyon bayan Tinubu a jihar, yayin da a gefe guda gwamnatin Radda ke gudanar da nata harkokin siyasa na jam’iyyar APC.

Wannan yanayi ya sa wasu ke ganin cewa akwai rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu, duk da cewa dukkansu suna cikin jam’iyyar APC.

Ana kuma zargin cewa magoya bayan ɓangarorin biyu na ƙara ruruta wutar rikicin, lamarin da ke sa wasu ke shakkar yiwuwar sasanta ɓangarorin kafin babban zaɓen 2027.

Rikici A Kan Fastocin Tinubu

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara jawo hankali shi ne kama wani matashin ɗan siyasa, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nasta, wanda ake danganta shi da ɓangaren Gwamna Radda.

An kama Nasta bisa zargin cire fastocin Shugaba Bola Tinubu.

Rahotanni sun kuma danganta kama shi da umarnin da ake zargin Ibrahim Masari ya bayar.

Daga baya an gurfanar da shi a gaban wata kotu a Abuja, inda aka tuhume shi da lalata fastocin Shugaban Ƙasa da kuma wani zargin da ya shafi kuɗi.

Daga bisani an bayar da belinsa.

Batun ya kuma kai ga gayyatar jami’an tsaron gidan Gwamnan Katsina, ciki har da ADC da CSO, zuwa shalkwatar ‘yansanda domin amsa tambayoyi kan lamarin.

Tun daga wannan lokacin, dangantakar siyasa tsakanin ɓangarorin biyu ta ƙara yin tsami.

A tarukan siyasa da kowanne ɓangare ke gudanarwa, ana ganin ƙarancin hulɗa ko halartar jami’an ɓangaren ɗayan.

Murabus Ɗin Jami’an Gwamnati

Ana cikin wannan yanayi ne aka fara ganin wasu jami’an gwamnatin Radda suna ajiye muƙamansu.

Tsohuwar Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Hajiya Hadiza Yar’adua, ta yi murabus bayan an sauya matsayinta daga kwamishiniya zuwa mai ba da shawara.

Ana alaƙanta ta da ɓangaren Ibrahim Masari.

Bayan haka, Abubakar Soja Tsanni, mai ba Gwamna shawara kan bunƙasa rayuwar al’umma, shi ma ya ajiye muƙaminsa tare da bayyana goyon bayansa ga tafiyar Ibrahim Masari.

Haka kuma, tsohon Sakataren Jam’iyyar APC na jihar a zamanin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, Barista Sulaiman Namadi, ya ajiye muƙaminsa na shugaban hukumar kula da zaizayar ƙasa ta jihar.

Daga baya, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Kabir Bature, wanda ake ganin yana da kusancin Gwamna Radda, shi ma ya yi murabus.

A ɓangaren mata kuma, Hajiya Fadila Sani Dalhatu ta ajiye muƙaminta na babbar mai taimaka wa gwamna kan ayyukan raya ƙasa, sa ido da tantancewa.

Haka kuma babban kwamandan Hisbah na jihar, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar), da mataimakinsa, Alhaji Muhammad Shitu Maslaha duk sun yi murabus, hakan ya ƙara tayar da hankalin masu bibiyar siyasar jihar.

Wasu Sun Fice Daga Jam’iyyar APC

Yayin da wasu daga cikin waɗanda suka ajiye muƙamansu suka bayyana goyon bayansu ga tsagin Ibrahim Masari, wasu kuma sun yi shiru kan makomar siyasarsu.

Akwai kuma wasu ‘yan siyasa da suka fice daga jam’iyyar APC zuwa wasu jam’iyyun siyasa, ciki har da PDP da ADC.

Ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Kankia, Hon. Salisu Rimaye, ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan takarar da suka rasa kujeru a zaɓen fidda gwani sun yi tunanin barin APC, yayin da wasu suka yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar.

Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa, rikicin siyasa a jihar Katsina da yadda yake shafar gwamnatin jihar da jam’iyyar APC na ci gaba da zama lamari mai jan hankali, musamman kan ko ɓangarorin Radda da Masari za su iya sasanta tsakaninsu ko kuma rikicin zai ci gaba da yin tasiri a siyasar jihar.

El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya
Rahotonni

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

October 20, 2026
Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Next Post
Ƙungiyoyi Sama Da 2,000 Sun Sauya Sheƙa Saboda Matsa Musu A Kaduna – Lawali

Ƙungiyoyi Sama Da 2,000 Sun Sauya Sheƙa Saboda Matsa Musu A Kaduna – Lawali

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.