Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba motoci 300 da babura 2,000 ga wasu ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane a jihar, yana mai cewa tallafa wa jama’a ba wai furuci kawai ba ne, illa samar musu da kayan aikin da za su taimaka musu dogaro da kansu da inganta rayuwarsu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin rabon motocin da baburan, wanda aka gudanar a Cibiyar Baje Kolin Kasuwanci da ke Gusau.
Shirin tallafin na da manufar karrama irin gudunmawar da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane suka bayar wajen ci gaban Jihar Zamfara baki ɗaya.

Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ne ya fitar da sanarwar a ranar 5 ga Nuwamba, 2026.
Gwamnatin jihar ta ce, rabon motocin da baburan na daga cikin shirinta na ƙarfafa tattalin arzikin al’umma, ta hanyar bai wa mutane da ƙungiyoyi damar shiga harkokin samar da kuɗaɗen shiga da kuma bunƙasa tattalin arzikin cikin gida.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya ce rabon kayayyakin na nuna wani sabon mataki ne a ƙoƙarin gwamnatin sa na farfaɗo da jihar, tare da karrama mutane da ƙungiyoyin da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban zamantakewa, tattalin arziki da siyasa.
Ya ce, “Na ji daɗin kasancewa a wannan taro domin ƙaddamar da rabon motoci ga wasu ɗaidaikun mutane da ƙungiyoyin siyasa da aka zaɓa a hankali daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara. Wannan taro na da muhimmanci matuƙa, domin ya ba ni damar miƙa motocin ga waɗanda aka zaɓa a hukumance.
“Ya kamata na jaddada cewa tallafa wa jama’a ya wuce furuci kawai. Yana nufin samar wa al’umma da ƙungiyoyin da ke matakin tushe da kayan aikin da za su taimaka musu dogaro da kansu, dawo da martabarsu da kuma amfana da ainihin romon dimokuraɗiyya.
“Muna nan daram kan aniyarmu ta tallafa wa al’ummar jihar wajen sake gina Zamfara da farfaɗo da ita, domin ta zama jiha mai wadata da ci gaba.
“Saboda haka, ina kira gare ku da kuka amfana da wannan tallafi da ku ci gaba da kasancewa masu jajircewa wajen mara wa ƙoƙarinmu na ceto al’ummar Zamfara baya. Gudummawar da kuke bayarwa wajen haɗin gwiwa da gwamnatin yanzu na da matuƙar muhimmanci.
“Yayin da za a miƙa muku motocinku a hukumance nan ba da jimawa ba, ina roƙonku da ku yi amfani da su yadda ya kamata. An samar da wannan tallafi ne domin sauƙaƙa zirga-zirga a faɗin jihar da kuma bunƙasa tattalin arzikin cikin gida.
“Gwamnatina za ta ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa ababen more rayuwa, farfaɗo da tattalin arziki da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tamu.”














