ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 6, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tallafin Tinubu: Cin Hanci Ko Taimako? Jam’iyyun Adawa Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Nuna Shakku

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 hours ago

Jam’yyun adawa da kungiyoyin farar hula sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ta fito da shirin tallafa wa al’umma a daidai lokacin da zaven 2027 ke kara gabatatowa tare da bayyana shirin a matsayin kokarin sayen kuri’un jama’a bisa hango faxuwa kasa.

A yayin da jam’iyyun adawa ke ikirarin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya assasa Shirin ne a bisa ga fargabar tsayuwar da suka yi wajen nuna masa kofar fita daga fadar mulki; kai tsaye kungiyoyin farar hula sun fassara tallafin a matsayin kokarin sayen kuri’un talakawa wadanda suka shekara suka shekara uku suna bukatar tallafi amma gwamnati ba ta tallafa masu ba sai daf da zabe.

Jam’iyyun adawa na ADC, NDC, APM da PDP sun bayyana tallafin a matsayin wata dabarar yaudara ta neman kuri’un al’ummar qasa a cikin gaggawa wanda a cewarsu hakan ya nuna fargabar jam’iyyar APC a karashin mulkin Tinubu gabanin zaben 2027.

ADVERTISEMENT

A kan wannan tuni matakin Gwamnatin Tarayya na fara biyan ma’aikatan gwamnati a dukkan matakai tallafin sufuri na naira 70,000 da kuma tallafin dubu 50, 00 ga talakawa wanda zai fara daga watan Nuwamba har tsayin watanni shida ya bayar baya da kura.

Tun da farko bayyana tallafin sufuri na daga cikin matsayar da aka cimma a taron sulhu tsakanin wakilan gwamnati da shugabannin Kungiyar Kwadago ta Kasa da aka gudanar a Abuja ranar Talatar makon jiya.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

A yayin taron bangarorin biyu sun tattauna kan walwalar ma’aikata, sabon mafi karancin albashi na kasa da kuma alawus-alawus da ake bin ma’aikata.Haka kuma, gwamnatin ta amince da biyan bashin alawus na musamman da ya kamata a fara biya tun daga ranar 1 ga Mayun 2026, inda za a biya kudin kashi-kashi har kashi uku daidai, tun daga watan Nuwamba. Sai dai bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan ranar da za a fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

A taron an amince cewa za a kafa kwamitin tattaunawa kan mafi qarancin albashi, wanda zai fara gudanar da taruka a nan take kamar yadda suka bayyana matsayar a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da aka fitar bayan taron wanda Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Muhammad Maigari Dingyaxi ya jagoranta.

Sai dai Kungiyar Kwadago ta TUC a karkashin jagorancin shugabanta, Festus Osifo ta yi watsi da tallafin sufuri na naira 70,000 ga ma’aikata domin a cewar kungiyar bayar da tallafin albashi na xan lokaci ba zai dore ba, kuma ba zai shafi yawan ma’aikata yadda ya kamata ba.

A maimakon haka, TUC ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta karawa ma’aikata albashi domin rage radadin tsadar rayuwa, a kan hakan kungiyar ta bukaci gwamnati ta biya mafi karancin albashi ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 300,000 a duk wata.

Haka ma gwamnatin tarayya ta bayyana cewar ta kammala shirin bayar da tallafin kudi na wata- wata ga masu qaramin qarfi wanda za a rika baiwa iyalan da ke cikin mawuyacin hali naira 50,000 domin rage musu radadin tsadar rayuwa.

Ministan Harkokin Jinqai da Rage Fatara, Bernard Doro ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’ar makon da ya gabata a Abuja, lamarin da tuni kungiyar kwadago ta TUC ta yi tsaye kan qarin albashin dubu 300, 000 shi ne mafita ba tallafi dubu 50 ba.

Kamar yadda Ministan ya bayyana gwamnatin tarayya ta fito da shirin na musamman da Shugaban kasa ya kaddamar domin baiwa miliyoyin ’yan Nijeriya masu fama da matsin rayuwa tallafin kudi cikin gaggawa.

Ya ce an kaddamar da shirin ne sakamakon hauhawar farashin abinci a duniya da kuma tsadar kayayyakin masarufi, lamarin da ke qara jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki, sai dai jam’yyun adawa sun bayyana cewar tun hawan gwamnatin Tinubu ‘yan kasa ke cikin matsi musamman bayan cire tallafin mai amma ba a saurari kukan su ba sai daf da zabe za a ba su tallafin da ba zai yi masu komai ba.

“A karkashin shirin, wadanda suka cancanci tallafin za su rika samun naira 50,000 a duk wata domin taimaka musu wajen biyan bukatun yau da kullum da kuma rage musu nauyin tsadar rayuwa.” In ji shi.

Ministan ya kuma ce za a rika duba shirin lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da cewa tallafin ya dace da sauye-sauyen farashin kayayyaki, inda ya kara da cewa za a sanar da wadanda za su amfana kai tsaye kafin yin duk wani sauyi.

A cewarsa, ma’aikatar tana aiki tare da kamfanonin samar da ayyukan kudi na zamani masu lasisi domin tabbatar da cewa a na aika kuxin cikin aminci, akan lokaci kuma a cikin gaskiya.

Ya bayyana cewa wadanda suka cancanci tallafin za su rika samun sakon waya daga kamfanonin da ke gudanar da shirin domin neman izininsu kafin aika kudin kai tsaye zuwa asusun bankunansu ko walet din su.

Duk da cewar jami’an ma’aikatar ba su bayar da cikakken bayani kan tsarin tantance wadanda za su amfana ba kafin lokacin kammala wannan rahoto. Sai dai binciken LEADERSHIP HAUSA ya nuna cewa ba a buqatar mutum ya nemi tallafin ko ya biya wani kudi, domin za a zabi wadanda za su amfana ne bisa tsarin tallafin jinkai da ake da shi a baya, ba tare da fayyace ka’idojin tantancewar ko ma’anar wadanda ake dauka a matsayin masu karamin karfi ba.

Tuni dai ’yan adawa da kungiyoyin farar hula suka nuna shakku kan shirin na Gwamnatin Tarayya na baiwa talakawa ’yan kasa tallafin naira 50,000 duk wata tare da nuna damuwa kan lokacin fito da shirin gabanin zaben 2027, yadda za a zabi wadanda za su amfana da kuma ko kudin zai iya rage musu radaɗin matsin tattalin arziki.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi watsi da tallafin, ya ce hakan ba zai magance matsin tattalin arziki da jama’a ke fama ba. Ya ce a yayin da farashin man fetur ke Naira 1,400 kan kowace lita, naira 70,000 za ta iya sayen man fetur kimanin lita 50 ne kacal.

Ya ce shirin tallafin bai shafi ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, ’yan kasuwa, masu kananan sana’o’i da kuma miliyoyin mutanen da ke aiki a bangaren tattalin arziki na yau da kullum ba tare da tsarin gwamnati ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen magance hauhawar farashin abinci, wutar lantarki, haya da sufuri domin biyan tallafi na dan lokaci ba zai maye gurbin ingantattun manufofin tattalin arziki masu xorewa ba.

A nata bangaren qungiyar kare hakkin fararen hula ta CISLAC ta gargadi Gwamnatin Tarayya da kada ta mayar da tallafin kudin wata hanya ta neman goyon bayan siyasa ko sayen kuri’u gabanin zaben 2027.

Haka kuma, wasu kungiyoyin farar hula sun bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki masu dorewa domin magance matsalolin da ke jefa ’yan Nijeriya cikin wahala.

Ƙungiyoyin sun amince cewa tallafin kudi na iya taimaka wa iyalan da ke cikin mawuyacin hali, amma sun ce bayar da kudi kadai ba zai magance tushen talauci ba. A kan wannan sun bukaci gwamnati ta ba da fifiko ga samar da ayyukan yi, saukaka samun abinci, zuba jari a harkar noma, inganta ababen more rayuwa da kuma samar da ayyukan jinkai ga al’umma cikin sauki.

Da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP Weekend a wata hira ta musamman, Daraktan kungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya nuna shakku kan lokacin da aka fito da shirin, yana mai cewa miliyoyin ’yan Nijeriya sun shafe kusan shekaru uku da rabi suna fama da matsin tattalin arziki ba tare da samun isasshen tallafi ba.

Ya tambayi dalilin da ya sa gwamnati ta fara nuna irin wannan gaggawa a yanzu da zabe ke gabatowa, alhali jama’a sun shafe tsawon lokaci cikin wahala ba tare da wani tallafi daga gwamnati ba.

Ita ma wata manba a kungiyar farar hula da ke zaune a Kaduna, Hadiza Umar, ta yi tambaya kan dalilin fito da shirin a daidai wannan lokaci da zaben 2027 ke qaratowa. Ta ce duk da cewa labari ne mai dadi jin gwamnati za ta ba da tallafin ga ’yan Nijeriya, amma akwai tambayoyi da dama da suka kamata gwamnati ta amsa.

Daga cikin tambayoyin da ta bukaci amsar su akwai dalilin fito da shirin a yanzu, wadanne mutane ne za a dauka a matsayin matalauta, yadda aka kayyade adadin naira 50,000, da kuma yadda za a gano wadanda suke bukatar tallafin da gaske.

A cewarta, abin damuwa shi ne kudin da za a bayar kudin haraji ne da ’yan kasa ke biya, don haka ya kamata a yi amfani da su yadda ya kamata domin amfanin kowa, musamman talakawa da masu rauni.

Bugu da kari jam’iyyun adawa na ADC da Allied Peoples Movement (APM) da kuma bangaren jam’iyyar PDP karqashin jagorancin Tanimu Turaki, sun soki shirin tare da bayyana cewar ko kaxan ba a fito da shirin a lokacin da ya dace ba alhali ‘yan kasa sun kwashe shekaru uku suna fama da tsadar rayuwa.

ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da kokarin dawo da amincewar jama’a ta hanyar raba tallafi, bayan abin da ta bayyana a matsayin tsananin matsin tattalin arziki da manufofin gwamnatin suka jefa ’yan Nijeriya a ciki.

A sanarwar da kakakin jam’iyya na qasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya sanyawa hannu, ADC ta nuna cewar fito da shirin tallafin a daidai lokacin da ake daf da zabe bai dace ba domin mataki ne na sayen kuri’un jama’a.Jam’iyyar ta yi zargin cewa matakin martani ne ga alkawarin da ta yi na rage tsadar rayuwa da kuma saukaka wa ’yan Nijeriya halin kuncin rayuwa da suke ciki idan ta samu nasara a zaben 2027.

A cewar jam’iyyar, gwamnatin ta sanar da shirin tallafi da dama a baya-bayan nan, amma ba a ga wani gagarumin sauki a rayuwar ’yan Nijeriya ba.

Jam’iyyar ta ce “Shugaba Tinubu ya shiga tsananin fargaba tun bayan da ADC da dan takararmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka mayar da saukaka tsadar rayuwa, dawo da tallafin man fetur ginshikan manufofin yakin neman zabensu, sai gwamnati ta fara bayyana shirin tallafi na gaggawa wani na bin wani wanda kuma ba wanda ya yi tasiri.”

Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027: Yadda ‘Yan Siyasa Ke Amfani Da Matasa A Bangar Siyasa
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Amince Da Kafa ’Yansandan Jihohi
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Kotu Ta Yankewa Jami’an Tsaron Sa- Kai 3 Hukuncin Kisa A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Majalisar Sarkin Musulmi Za Ta Kafa Bankin Musulunci Don Yaƙi Da Talauci

MASU ALAKA

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano
Labarai

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

November 6, 2026
ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi
Labarai

ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

November 6, 2026
Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa
Manyan Labarai

Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

November 6, 2026
Next Post
Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano

November 6, 2026
ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

November 6, 2026
Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

Sin Tana Sahun Gaba Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Wajen Bude Kofarta Ga Ketare

November 6, 2026
Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

Ƴan Adawa Sun Zargi APC Da Yi Wa Dimokuraɗiyya Ƙanshin Mutuwa

November 6, 2026
Tallafin Tinubu: Cin Hanci Ko Taimako? Jam’iyyun Adawa Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Nuna Shakku

Tallafin Tinubu: Cin Hanci Ko Taimako? Jam’iyyun Adawa Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Nuna Shakku

November 6, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Jigon “Jagorancin Kasar Sin Da Ci Gaban Duniya” A Kuwait

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Jigon “Jagorancin Kasar Sin Da Ci Gaban Duniya” A Kuwait

November 5, 2026
Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

Obi Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Soke Takarar Atiku A ADC

November 5, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

Gwamnan Zamfara Ya Raba Motoci 300 Da Babura 2,000 Ga Ƙungiyoyi Da Ɗaiɗaikun Mutane A Gusau

November 5, 2026
Wang Huning Ya Yi Kira Ga Mabiya Addinin Dao Su Ba Da Gudunmuwa Ga Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Dan Adam

Wang Huning Ya Yi Kira Ga Mabiya Addinin Dao Su Ba Da Gudunmuwa Ga Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Dan Adam

November 5, 2026
Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

Ra’ayin Sin Game Da Kimiyya Da Fasaha: Bude Kofa Ga Juna Da Kuma Amfanar Da Kowa

November 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.