A wannan duniya ta yau mai fuskantar tarin kalubalen aiwatar da manufofin kare yanayi, inda wasu sassa ke rungumar manufofin kare kai daga sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, da tarin kalubalen samar da isasshen makamashi mai inganci, daukacin bil’adama na matukar bukatar a aiwatar da manufofi na hakika, wadanda za su mara baya ga yarjejeniyar kare muhalli ta Paris.
Tun bayan fara aiwatar da wannan muhimmiyar yarjejeniya shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta ci gaba da ingiza matakan ragewa, da kawo karshen fitar da hayakin carbon mai dumama yanayi, wani mataki da duniya ta yi ittifakin gudummawa ce mai kima a fannin sauya akala zuwa turbar samar da ci gaba marar gurbata yanayi, da karfafa gwiwar dukkanin sassa wajen cimma nasarar samar da ci gaba marar gurbata yanayi.
Kasar Sin tana ci gaba da samar da gudummawar daidaita ayyukan kare yanayin duniya tun daga tushe a cikin gida, musamman yadda take aiwatar da tsarin dunkule hanyoyin samar da makamashi masu tsafta daga dukkanin fannoni. Wasu alkaluma na hukumar kasa da kasa mai lura da makamashi da ake iya sabunta amfani da shi ko IRENA, sun nuna yadda a shekarar 2025, Sin ta samar da gudummawar kusan kaso uku cikin hudu na jimillar sabon makamashin lantarki na duniya da ake samu daga karfin iska.
Masharhanta na ganin sauyi zuwa ga turbar ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba na bukatar abubuwa da dama, baya ga fasahohi akwai kuma bukatar samar da rahusa, da hajojin bukata a fannin wadanda za su dace da yanayin sassan duniya daban daban.
Kuma a wannan bangare kasar Sin ta ciri tuta.A cewar hukumar IRENA, farashin makamashi da ake samu daga karfin iska da hasken rana ya ragu da sama da kaso 60 da 80 bisa dari cikin shekaru 10 da suka gabata, ana kuma alakanta hakan da salon kirkire-kirkire na kasar Sin, da himmar masana’antun kasar na wannan fanni.
Kazalika, kasar Sin ta ci gaba da aiki tukuru wajen bunkasa hadin gwiwar kare yanayi, ta amfani da fifikonta a fannin fasahohi da jarin da take ci gaba da zubawa a fannin. Ga misali, a kasar Afirka ta kudu, Sin ta gina cibiyar samar da lantarki ta hasken rana mai lakabin “Redstone”, cibiyar da ta yi matukar taimakawa wajen saukaka karancin lantarki a kasar.
A ganin masana, ba wata kasa guda da za ta iya kammala dukkanin ayyuka masu nasaba da sauya akala zuwa samar da ci gaba marar gurbata yanayi. Wato dai akwai bukatar dukkanin kasashe su rungumi tsarin hadin gwiwa, da tafiya tare ta yadda za a iya kaiwa ga magance tarin kalubalen dake addabar tsarin jagorancin magance sauyin yanayi. (Saminu Alhassan)














