Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna damuwa kan hukuncin kotun da ya soke zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Obi ya ce hukuncin na iya haifar da ruɗani ga jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen ƙasar.
A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.
Kotun ta kuma soke duk matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Obi ya ce yana mutunta ikon kotu na yanke hukunci, amma yana fargabar cewa rashin tabbas kan ’yan takara da jam’iyyun siyasa na iya shafar zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.
Ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da haddasa rikice-rikice a jam’iyyun adawa, yana mai cewa irin waɗannan matsaloli sun shafi jam’iyyar Labour Party wadda ya yi takara a cikinta a baya.
Obi ya yi kira da a kare dimokuraɗiyya ta hanyar bai wa jam’iyyun adawa damar gudanar da harkokinsu da shiga zaɓe cikin ’yanci ba tare da tsoma baki ba.
Ya ce ya kamata masu kaɗa ƙuri’a ne su zaɓi shugabannin ƙasar, ba rikice-rikicen shari’a ba.
A halin da ake ciki, ADC ta sanar da shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin, yayin da Atiku ma ya sha alwashin ƙalubalantar hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara.














