A yau Alhamis ne aka kaddamar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 9 a birnin Shanghai.
Mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar Sin, Ding Xuexiang, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Ya kuma gana da manyan jamian kasashe daban-daban da suka halarci bikin bude baje kolin.
Rahotanni na cewa baje kolin na CIIE zai gudana ne tun daga yau 5 zuwa ranar 10 ga watan nan na Nuwamba, kuma ya hallara masu baje hajoji na kasashen ketare 4,142, yayin da jimillar fadin wurin baje kolin ya haura sakwaya mita 440,000. Har ila yau, ana sa ran yayin baje kolin na wannan karo, sama da masu baje hajoji 480 za su gabatar da kayayyakinsu a karon farko, a ko dai matakin kasa da kasa, ko a nahiyar Asiya ko kuma a kasar Sin, adadin da zai zamo mafi girma da aka taba samu a tarihi.
Adadin kamfanonin ketare da manyan masanaantu da suka halarci baje kolin kasa da kasa, na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 9 sun yi matukar karuwa tare da kafa sabbin tarihi, wanda hakan ke nuni ga karbuwa da baje kolin mafi girma na hajojin da ake shigarwa wata kasa ke samu.
Baje kolin na CIIE na wannan karo ya kuma samu halartar kamfanoni sama da 300 cikin 500 mafiya girma a duniya, da kuma tarin wakilan manyan masanaantu da ake sa ran za su halarta, a wani yanayi na kafa sabon tarihin bunkasar baje kolin. Kari kan hakan, mashirya baje kolin sun ce ana sa ran sama da kamfanoni 2,000 za su baje hajojinsu a karon farko a wannan lokaci.
Baje kolin CIIE muhimmin misali ne na jerin kokari da kasar Sin ke yi, wajen kara bude kasuwarta, da ingiza shigo da hajoji masu nagarta daga sassan duniya daban daban. Kasar Sin na fatan fadada shigo da hajoji domin bunkasa bukatun cikin gida, da tallafawa manufar daga darajar masanaantunta. A watanni tara na farkon shekarar bana, darajar hajojin da Sin ta shigo da su daga ketare ta kai dalar Amurka tiriliyan 2.48, adadin da ya karu da kaso 22.3 bisa dari, saurin karuwa mafi girma da kasar ta samu tun bayan shekara ta 2021. (Saminu Alhassan)













