Jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da jefa zaman lafiya da kwanciyar hankalin Nijeriya cikin hatsari ta hanyar yunƙurin raunana jam’iyyun adawa.
Jam’iyyar ta yi wannan zargi ne bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar Alhamis, wanda ta rushe shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark tare da soke takarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce hukuncin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan ɗimbin magoya bayanta sun halarci gangamin yaƙin neman zaɓenta a Sakkwato.
Jam’iyyar ta gargaɗi APC kan amfani da kotu wajen kawar da hamayya a siyasa, tana mai cewa bai kamata tsananin son yin mulki ya jefa zaman lafiyar ƙasar cikin hatsari.
ADC ta kuma buƙaci mambobinta su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda yayin da ta ke shirin ƙalubalantar hukuncin ta hanyar shari’a.













