Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Huning, ya yi kira ga mabiya addinin Dao da ke fadin duniya, su bayar da gudunmuwa ga wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya da ma gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dan Adam.
Wang Huning, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, ya yi kiran ne cikin sakon taya murna ga taron kasa da kasa na 6 na mabiya addinin Dao da aka kaddamar yau Alhamis a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na gabashin kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














