Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da ware Naira biliyan 1.65 domin gyaran Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Birgediya Zakari Maimalari da kuma girka fitulun titi masu amfani da hasken rana a kan hanyar da ta haɗa filin jirgin saman da sauran hanyoyin filin.
An amince da kuɗaɗen ne a taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Gombe karo na 55 da aka gudanar ranar Juma’a, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
A ƙarƙashin shirin, Majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 414.3 domin gyara wuraren da ambaliyar ruwa ta lalata a filin jirgin saman sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a baya-bayan nan.
Haka kuma, an amince da Naira miliyan 839.5 domin gyaran gine-gine da samar da kayan aiki a filin jirgin saman, ciki har da gyaran muhimman abubuwan more rayuwa da kuma samar da motocin kashe gobara na filin jirgin.
Kwamishinan Gidaje da Raya Birane, Muhammad Saidu Fawu, ya bayyana cewa Majalisar ta kuma tabbatar da kwangilar Naira miliyan 400.5 domin saye da girka fitulun titi masu amfani da hasken rana guda 198 a kan hanyar da ta kai tsawon kilomita huɗu, wadda ta haɗa Sansanin Alhazai da filin jirgin saman, ciki har da hanyoyin cikin filin jirgin.














