Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana cewa, ta na bai wa harkar noman Auduga muhimmanci, musamman domin ta kara bunkasa fannin a daukacin fadin jihar, samar da ayyukan yi ga ‘yan jihar, kara habaka tattalin arzikin jihar da kuma kara bai wa manomanta kwarin guiwa.
Furuncin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Aikin Gona na Jihar, Muhammad Magaji Gettado a jawabinsa a lokacin want taro da aka gudanar a kwanan baya a jihar akan yadda za a kara bunkasa fannin, musamman a jihar.
- Takaddamar Da Ta Kunno Kai Lokacin Tantance Ministocin Tinubu
- Gwamna Dauda Ya Karbi ‘Yan Mata Hudu Da Suka Kwashe Watanin 7 A Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara
A cewarsa, a baya manoman na Audugar a jihar sun funaci matsaloli, inda ya bayyana cewa, amma tuni gwamnatin jihar ta magance wadanan natsalolin, musamman ganin yadda ta samar wa manomanta kayan aikin noma na zamani da sauransu
Magaji ya kara da cewa, akwai kuma bukatar a ilimantar da manomata, musaman wajen samar masu da ingantacce Iri wanda hakan zai taimaka masu don su kara bunkasa noman na su na Audgar a jihar.
A cewarsa,”Gwamnatin Jihar ta na bai wa harkar noman auduga muhimmanci kasancewar ta fanni ne da ke kara bunkasa tattalin arziki. “
Shi kuwa a na sa jawabin a matsayin babban bako a wajen taron shugaban kungiyar manoman Auduga na kasa Alhaji Lawan Sani Matazu, ya bayyana cewa, a watannin da suka gabata, kungiyar ta kaddamar da shirin habaka noman Auduga a jihar, wanda ya ce, waccan kaddamar kwaliya ta but ya kudin Subulu, musamman ganin cewa, fannin na kara bunkasa a jihar.
A cewarsa, jihar ta Gombe kusan a daukacin fadin kasar nan, ita ce ke a gaba wajen noman auduga, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ci gaba da bai wa fannin mahimmanci domin jihar ta ci gaba da rike wannan kambun na ta.
” A watannin da suka gabata, kungiyar ta kaddamar da shirin habaka noman Auduga a jihar, wanda ya ce, waccan kaddamar kwaliya ta but ya kudin Subulu, musamman ganin cewa, fannin na kara bunkasa a jihar. “
Matazu, ya ce noman Auduga hanyar ci gaba ne ga matasa domin, fannin na samar da aikin yi da kuma kudin shiga, musamman ga manoman da suka rungumi fannin ka’in da na’in.
Ya buga misali da cewa, ingantacce Irin nomanta da Babban Bankin Nijeriya CBN, ya rabarwar da wasu manomanta ‘ya’yan kungiyar a jihar ta Gombe, hakan ya kara taimaka wa wajen kara bunkasa nomanta a jihar da kuma kasa baki daya.
“Ingantacce Irin nomanta da Babban Bankin Nijeriya CBN, ya rabarwar da wasu manomanta ‘ya’yan kungiyar a jihar ta Gombe, hakan ya kara taimaka wa wajen kara bunkasa nomanta a jihar da kuma kasa baki daya. “
Kazalika ya bayyana cewa,bashin, da bankin ya bai wa manomanta a jihar shi ma ya taimaka wajen bunkasa sana’ar su da kara samar wa da kansu da kudaden shiga.
Shugaban ya kuma yi kira ga manomanta da su tabbatar da suna shuka ingantacce irin na Audugar domin su dinga samun dimbin kudaden shiga da kuma samun amfani mai yawa idan sun yi girbi.
” Ina kira ga manomanta da su tabbatar da suna shuka ingantacce irin na Audugar domin su dinga samun dimbin kudaden shiga da kuma samun amfani mai yawa idan sun yi girbi. “