Gwamnatin Jihar Kano ta mika ‘School of Rural Technology and Entrepreneurship Development, Rano’, ga kwamitin da ke kula da shirye-shiryen kafa sabuwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da aka tanada.
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika makarantar ne a ranar Juma’a, lokacin da ya gana da mambobin kwamitin tare da duba kayayyakin aiki da aka tanada domin fara aikin sabuwar makarantar.
Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin ganin an kafa makarantar cikin nasara tare da tabbatar da fara ayyukanta cikin gaggawa.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ilimin fasaha da koyar da sana’o’i wajen shirya matasa domin samun ayyukan yi, dogaro da kai da kuma bunkasa harkokin kasuwanci.














