Hukumar Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ta Ƙasa (NDLEA) ta bayyana cewa jami’anta sun kama wata tsohuwa mai shekara 101 a Jihar Ogun wacce ake zargi da sayar da miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi.
Hukumar ta kuma sanar da gano wasu ƙunshin hodar iblis da aka ɓoye a cikin fufu a wani farmaki da suka kai a Jihar Akwa Ibom. Daraktan Yaɗa Labarai na hukumar, Femi Babafemi, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a madadin hukumar.
A cewar sanarwar, an kama tsohuwar mai suna Esther Ogunmabo a garin Ilisan da ke Jihar Ogun a ranar 15 ga watan Agusta, 2026, ɗauke da giram 90 na tabar wiwi ƙirar skunk da aka ƙunshe domin sayarwa. Yayin da take amsa tambayoyi, tsohuwar ta shaida wa jami’an cewa ta fara sayar da ƙwayoyin ne bayan wata gobara ta cinye mata shagon kayan masarufinta, inda ta tabbatar da cewa wata ƴarta da ke Legas ce ke kawo mata saƙon duk bayan kwanaki huɗu domin ta sayar a yankinsu.
Sakamakon yawan shekarunta, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai murabus), ya ba da umarnin a bayar da belinta nan take tare da sanya ta a ƙarƙashin shirin ba da shawarwari, inda a ɗaya ɓangaren kuma aka damƙe ƴarta ta don fuskantar shari’a.














